'Yadda Na Roki Abacha Afuwa domin Ceto Ran Obasanjo': Tsohon Shugaban Kasa Ya Magantu
- Janar Yakubu Gowon ya bayyana yadda ya ceto rayuwar tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo
- Gowon ya ce ya roki marigayi Sani Abacha da ya yi afuwa ga Obasanjo kan zargin hannu a juyin mulki a 1995
- Tsohon shugaban kasar ya ce ya rubuta takarda musamman ga Abacha inda yake rokon ya yi masa afuwa kan zarginsa da ake yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Plateau - Tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon ya fadi yadda ya taimaki rayuwar Olusegun Obasanjo.
Janar Gowon ya bayyana yadda ya roki marigayi Sani Abacha ka da ya hukunta Obasanjo saboda zargin juyin mulki a 1995.
Yadda aka tsare Obasanjo kan zargin juyin mulki
Tsohon shugaban kasar ya yi wannan jawabi ne a yau Asabar a wani babban taro da gwamnatin Plateau ta shirya, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ba a mantaba, a shekarar 1995 Abacha ta cafke Obasanjo kan zargin juyin mulki don neman kifar da gwamnatinsa.
Duk da roko da kuma neman wanke kansa da Obasanjo ya yi, sai da aka yanke masa hukuncin kisa.
Obasanjo ya shafe shekaru uku a gidan kaso kafin sakinsa a 1998 bayan mutuwar Sani Abacha, TheCable ta ruwaito.
Gowon ya ce ya rubuta wasika ga Abacha inda ya roke shi kan yiwa Obasanjo afuwa kan zargin juyin mulki.
Yadda Gowon ya yi kokarin ceto ran Obasanjo
"Na rubuta wasika ga Abacha inda na roke shi kan cewa Allah ya ba shi mulki ne domin ya yi abin kirki ba na banza ba."
"Na tura matata da takarda zuwa Abuja da tsakar dare, na roke shi kan cewa bai kamata hakan ta faru ba."
"Na yi farin ciki bayan lokaci kadan, Obasanjo ya fito daga gidan yari har ma ya mulke mu a 1999."
- Janar Yakubu Gowon
Gowon ya fadi dalilin kirkirar jihohi
Kun ji cewa Janar Yakubu Gowon ya bayyana cewa kirkiro jihohi 12 ya taimaka wajen rage tashin hankali da kawar da tsoron mamayar Arewa.
Tsohon shugaban kasar ya yi wannan bayanin ne yayin ziyarar kungiyar Sanata Ibrahim Shekarau a cibiyarsa da ke Abuja.
Gowon ya yi kira ga shugabannin Arewa da su fifita muradun Najeriya, yana mai cewa hadin kai shi ne tushen dorewar dimokuradiyya.
Asali: Legit.ng