Kudirin Haraji: Sanata Ali Ndume Ya Yi Barazanar Ficewa daga Jam'iyyar APC

Kudirin Haraji: Sanata Ali Ndume Ya Yi Barazanar Ficewa daga Jam'iyyar APC

  • Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa kusancinsa da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ne kaɗai ya riƙe shi a jam'iyyar APC
  • Ndume ya ce a shriye yake ya sauya sheka daga APC ci mulki idan shugabanni suka ba shi damar hakan saboda kudirin haraji
  • Ya ce baya goyon bayan kudirin ne saboda duk wahalar a kan talakawa za ta kare domin kamfanoni za su kara kudin kayansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Sanatan Borno ta Kudu, Muhammad Ali Ndume, ya ce a shirye yake ya bar APC mai mulki idan har shugabancin jam’iyyar suka ba shi damar hakan.

Sanata Ndume ya ce tun kafin yanzu ya yi niyyar ficewa daga APC amma ya haƙura saboda kyakkyawar alaƙarsa da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Ali Ndume.
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa kusancinsa da Tinubu ya hana shi barin APC Hoto: Mohammed Ali Ndume
Asali: Twitter

Ndume ya jaddada cewa ko kaɗan ba ya ƙaunar shugaba Tinubu ya gaza yin abin da ƴan Najeriya ke bukata a tsawon zangon mulkinsa.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta tafka muhawara, kudirin harajin Tinubu ya tsallake karatu na 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ali Ndume ya yi barazanar barin APC

Ali Ndume ya bayyana haka ne ranar Alhamis a wata hira da gidan talabijin na Channels kan sabon kudirin sauya fasalin haraji.

Sanatan ya ce:

"Na faɗa maku ina da kusanci da Shugaba Tinubu, ba na son ya gaza shiyasa nake ɗaukar zage-zagen da ake mani, ba don haka ba zan iya barin jam'iyyar.
"Zan iya tattara kayana na fice daga jam'iyyar, dama an mani tayi a baya cewa na tafi idan ina so, don haka zan iya tuna masu idan suka amince sai na kama gabana."

"Komai kan talaka zai ƙare" - Ndume

Dangane da batun kudirin haraji kuma, Sanata Ndume ya misalta lamarin da bai wa mutum kyauta da hannun dama kuma ka dawo ka karbi abinka da na hagu, Premium Times ta kawo.

Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin dalilin da ya sa bai yarda da sabon kudurin ba shi ne za su ƙara jibga haraji kan kamfanoni ta yadda su kuma za su ƙara tsadar kayayyakin su.

Kara karanta wannan

Mutumin Gombe da ya niƙi gari ya tafi Abuja a keke ya samu kyautar mota da kudi

"Idan ta ƙarawa Ɗangote haraji a kan man da yake tacewa a matatarsa, haƙan na nufin dole ya kara farashin lita," .

- Ali Ndume

Kudirin haraji: Sanatocin Arewa sun sa labule

A wani rahoton, an ji cewa Sanatocin Arewa sun gudanar da taron sirri a ranar Alhamis bayan kudurin dokar gyaran haraji ya tsallake karatu na biyu.

Sai dai ba a gano abin da ganawar ta kunsa ba, yayin da shugaban kungiyar, Sanata Abdulaziz Yar'Adua ya ki cewa komai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262