Jagora a PDP Ya Fusata, Ya 'Fallasa' Masu Kunno Mata Rigimar cikin Gida a Kano
- Jam'iyyar PDP a Kano ta bayyana takaicin yadda APC ke aiki tukuru wajen kawo mata rikicin cikin gida
- Kusa a APC, Aminu Wali ya ce ba haka kawai PDP ke fadawa a cikin mawuyacin halin da ta ke ciki ba
- Sai dai APC ta yi martani, ta zargi PDP da watsa tafiyarta a maimakon mayar da hankali wajen kawo gyara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Guda daga cikin wadanda suka kafa PDP, Aminu Wali, ya zargi jam’iyyar mai mulki, APC da ƙara rura rikicin cikin gida a PDP.
Ambasada Aminu Wali ya yi iƙirarin cewa da gangan APC ke haddasa rarrabuwar kawuna a cikin jam’iyyun adawa domin lalata tsarin siyasar ƙasa.
A wata hira da ya yi da BBC, Wali, kusan a PDP ya bayyana cewa babu shakka jam’iyyarsata fada rikicin cikin shiga ne a yanzu, saboda shishshigi na ‘yan adawa, musamman APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar PDP ta gano APC na yi mata katsalandan
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jigo a APC, Aminu Wali ya ce ba za su bar jam'iyyar adawa ta yi nasara wajen rikita 'yan PDP ba.
Ya bayyana cewa duk da APC ba ta shiga harkokinta kai tsaye, ta na bi ta karkashin kasa wajen rura wutar rikicin da ke addabar ta.
APC ta musanta hannu a rikicin cikin gidan PDP
Jami'in hulda da jama'a na APC a Kano, Ahmed Aruwan ya musanta cewa su na da hannu a cikin matsalolin cikin gida da ya dabaibaye su ba
A cewar Ahmed S Aruwan;
"Su (PDP) sun fi neman laifuffuka a maimakon mayar da hankali kan sake gina jam'iyyarsu."
Ba wannan ne karon farko da PDP da wasu jamiyyun ke zargin APC da cewa ta na hannu a cikin haddasa mata rikici ba.
Wasu 'ya 'yan APC sun koma PDP
A baya mun ruwaito cewa wani daga cikin ƙusoshin APC a jihar Bauchi, Adamu Bello ya tattara kayansa zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.
'Dan siyasar ya kara da cewa zai yi kokarin jawo da yawa daga cikin magoya bayansa zuwa PDP domin kara mata karfi wajen ganin ta gwabza da yan adawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng