Kwankwaso Ya Tsoratar da Tinubu, Ana Zargin EFCC Ta Fara Bincike domin Karya Shi
- Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa hukumar EFCC ta fara binciken jam'iyyar NNPP kan kudin yakin neman zaben 2023
- Ana hasashen an kaddamar da binciken ne saboda ragewa jagoran jam'iyyar, Rabiu Kwankwaso karfi musamman a zaben 2027
- Hakan ya biyo bayan caccakar Bola Tinubu da ya yi da kuma tasirinsa musamman lokacin da ya aurar da yarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Yan Najeriya da dama na zargin hukumar EFCC da neman rufe bakin yan adawa a kasar.
Hukumar yaki da cin hanci ga fara gudanar da bincike kan halaccin kudin kamfe na jam'iyyar NNPP a kasar.
Kwankwaso ya zargi Tinubu da mulkin mallaka
Wasu na ganin binciken NNPP wani yunkuri ne na durkusar da Sanata Rabi'u Kwankwaso musamman saboda zaben 2027, cewar Daily Nigerian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan bai rasa nasaba da caccakar gwamnatin Bola Tinubu da Kwankwaso ya yi na zargin kokarin mulkin mallaka a yankin Arewa.
Kwankwaso ya yi zargin cewa akwai shirin yi wa Arewa mulkin mallaka da Lagos ke yi wanda har ikon naɗa sarki ba za su samu damar yi ba.
Har ila yau, wasu sun ce Gwamnatin Tarayya ta tsorata duba da gagarumin taro da kuma halartar manyan mutane bikin yar jagoran NNPP a Kano.
Ana zargin EFCC ta fara binciken Kwankwaso
Wata majiya ta ce hukumar EFCC ta fara binciken ne bayan korafi da wasu fusatattun 'yan jam'iyyar NNPP da aka kora suka yi.
"An umarci hukumar EFCC ta fara binciken Rabiu Kwankwaso kan kudin kamfen zaben 2023 na NNPP."
"An bukaci ta neme shi domin ya amsa tambayoyi bayan wasu fusatattu da aka sallama a jam'iyyar sun shigar da korafi."
- Cewar wata majiya
Ministan Tinubu ya yi wa Kwankwaso raddi
Kun ji cewa karamin ministan gidaje da raya birane ya yi martani kan kalaman da Rabiu Musa Kwankwaso ya yi na shirin durƙusar da Arewa.
Hon. Yusuf Abdullahi Ata ya buƙaci jagoran na jam'iyyar NNPP na ƙasa da ya guji yin kalaman da za su iya kawo tashin hankali a yankin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng