Jam'iyyar PDP Ta Dakatar da Dan Majalisa, Ta Fadi Laifinsa
- Jam'iyyar PDP ta dakatar da ɗan majalisar dokokin jihar Bauchi, mai wakiltar ƙaramar hukumar Kirfi
- PDP ta aika wasiƙar dakatar da Habibu Umar har sai baba ta gani ga shugaban majalisar dokokin jihar, bisa zarginsa da laifin rashin biyayya
- An dakardar da ɗan majalisar dokokin ne bayan kwamitin da aka kafa domin bincike kan zargin da ake masa ya ba da shawarar a hukunta shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bauchi - Jam’iyyar PDP a Bauchi ta dakatar da ɗaya daga cikin ƴan majalisunta na majalisar dokokin jihar.
Jam'iyyar PDP ta dakatar da ɗan majalisar da ke wakiltar ƙaramar hukumar Kirfi, Habibu Umar, saboda zargin rashin biyayya.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata wasika da ya aike wa kakakin majalisar dokokin jihar, Abubakar Sulaiman, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasiƙar dakatar da ɗan majalisar na ɗauke da sa hannun shugaban jam’iyyar PDP na jihar Bauchi, Sama’ila Burga
Meyasa PDP ta dakatar da ɗan majalisa?
"An miƙawa Habibu Umar takardar jin ba'asi mai ɗauke da kwanan watan 5 ga watan Nuwamba, bisa laifin rashin biyayya wanda ya saɓawa sashe na 58 (9) (1) da (f) na kundin tsarin mulkin jam'iyya na 2017 wanda aka yi wa kwaskwarima."
"Bayan hakan, an kafa kwamitin ladabtarwa a ranar, 11 ga watan Nuwamba, kamar yadda kundin tsarin mulkin jam'iyya ya tanada."
"Kwamitin, bayan gudanar da bincike, ya samu ɗan majalisar da laifin da ake zarginsa, tare da ba da shawarar dakatar har sai baba ta gani nan take."
- Sama'ila Burga
Ya yi nuni da cewa sakamakon hakan, daga ranar, 25 ga watan Nuwamban 2024 an haramta masa shiga kowace harka da ta shafi jam'iyyar, rahoton The Guardian ya tabbatar.
An tattaro daga majiyoyi cewa an dakatar da Umar Habibu ne bisa zargin ɗasawa da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.
Kusa a APC ya koma PDP a Bauchi
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta rasa ɗaya daga cikin manyan jiga-jiganta a jihar Bauchi, Adamu Bello ya koma PDP.
Adamu Bello, wanda tsohon ɗan majalisar jiha ne kuma tsohon shugaban ƙaramar hukumar Giade, makusanci ne ga Saddique Baba Abubakar, ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APC a zaɓen 2023.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng