'Babu Yadda Za a Yi Shugabancin Najeriya Ya Dawo Hannun Mutanen Arewa," Okupe
- Tsohon hadimin Cif Olusegun Obasanjo ya fadi dalilin da ya sa mulkin kasar nan ba zai dawo hannun 'yan Arewa a 2027 ba
- Ya bayyana cewa akwai wata yarjejeniya da ba a rubuta ba, wacce ta tabbatar da mulkin karba karba tsakanin shiyyoyin
- Doyin Okupe ya na wannan batu ne yayin da aka fara samun wasu manyan Arewa da kokarin maido mulki yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Tsohon hadimin shugaban kasa, Doyin Okupe, ya bayyana cewa shugabancin Najeriya ba zai koma yankin Arewa a zaben 2027 ba.
Ya bayyana haka ne a ranar Litinin, inda ya danganta haka da abin da ya faru kafin Olusegun Obasanjo ya hau mulki a 1999.
Arise Television ta wallafa cewa Okupe ya ce akwai wata “yarjejeniya marar rubutu” domin samar da shugabanni daga yankin Kudu maso Yamma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce an yi hakan ne domin kwantar da hankulan yankin bayan soke zaben 1993 da mutuwar MKO Abiola.
‘Babu zancen Arewa ta yi mulki,’ Okupe
Jaridar The Cable ta wallafa cewa tsohon hadimin shugaban kasa ya ce akwai dalilin da ya sa Arewa ba za ta yi mulki a 2027 ba.
Okupe ya ce;
“A gaskiya, akwai manyan masu ruwa da tsaki a wannan kasa, kuma tun daga 1960 an tsara yadda ake tafiyar da al’amura.
“Ko da yake ba mu yi nisa ba a fannin tattalin arziki, amma a siyasa mun tafiyar da kasa ta yadda har yanzu tana nan dunkulalliya.
Okupe ya fadi zabinsa a shugabancin Najeriya
Tsohon mai Magana da yawun Olusegun Obasanjo ya bayyana wanda ya ke ganin shi ne zai cigaba da jagorancin kasar nan.
A cewarsa, ba lallai sai shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma mulki ba, amma dole sai wanda ya fito daga Kudancin kasar nan ne zai zama shugaban kasa,
Ana son mulkin Najeriya ya dawo Arewa
A wani labarin kun ji cewa kungiyar tafiyar siyasa a Arewa, karkashin jagorancin tsohon gwamna, Malam Ibrahim Shekarau ta yunkuro domin maido da mulki shiyyar.
Kungiyar mai suna League of Northern Democrats ta fara tattaunawa da manyan kungiyoyi a Arewacin Najeriya domin gano yadda za a bullowa lamarin shugabanci da siyasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng