Gwamna Ya Ɗauki Zafi, Ya Dakatar da Kwamishinoni 2 da Wasu Hadimai a Ebonyi
- Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi ya dakatar da wasu kwamishinoni biyu daga aiki kan zargin rashin ɗa'a da sakacin aiki
- Kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Jude Chikadibia-Okpor ya bayyana hakan a sanarwar da aka rabawa manema labarai
- Ya ce gwamnan ya kuma dakatar da babban sakataren ma'aikatar lafiya da shugabannin hukumomi biyu na ɓangaren kiwon lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya dakatar da kwamishinoni biyu daga aiki kan wasu zarge-zarge da ake yi masu na rashin ɗa'a.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a na jihar Ebonyi, Jude Chikadibia-Okpor ya fitar ranar Talata.
Gwamna Nwifuru ya dakatar da kwamishinoni 2
A sanarwar kamar yadda Channels tv ta ruwaito, Gwamna Nwifuru ya dakatar da kwamishinan harkokin gidaje da raya birane, Injiniya Francis Ori har sai baba ta gani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Nwifuru ya kuma dakatar da kwamishinan lafiya, Dr. Moses Ekuma na tsawon watanni uku, The Nation ta ruwaito.
Gwamna ya dakatar da wasu hadimansa
"Sauran waɗanda gwamna ya dakatar na watanni uku sun haɗa da babban sakataren ma'aikatar lafiya, shugaban hukumar kiwon lafiya a matakin farko da takwaransa na hukumar inshorar lafiya.
"Saboda haka an umarci mai taimakawa gwamna kan harkokin kiwon lafiya a matakin farko ya karɓi ragamar kula da ma'aikatar lafiya a lokacin da dakataccen kwamishinan ba ya nan."
- Jude Chikadibia Okpor.
A cewar Okpor, an umurci waɗanda aka dakatar da su mika kayan gwamnati da ke hannunsu, ciki har da motoci ga sakataren gwamnati kafin tashi aiki a ranar Litinin 25 ga watan Nuwamba.
A baya dai Gwamna Nwifuru ya dakatar da kwamishinan albarkatun ruwa, Chinedum Nkah har sai baba ta gani bisa zargin sakaci da aikinsa.
Gwamnan jihar Ebonyi ya sa a kama ma'aikata
A wani labarin, an ji cewa Gwamnan Ebonyi, Francis Nwifuru, ya ba da umarnin cafke ma’aikata shida kan karkatar da takardun ma’aikatar lafiya.
An cafke ma'aikatan su na loda takardun da suka haɗa da rajistocin rigakafi da na haihuwa a cikin motoci da niyyar sayar da su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng