2027: Tinubu Zai Iya Ganin Adawar da Bai Taba Gani ba a Siyasa, Ana Shirin Kifar da Shi
- Sake neman takarar Bola Tinubu a zaben 2027 na cigaba da fuskantar matsaloli daga jam'iyyun adawa da kuma sauran kungiyoyi
- Jam'iyyun adawa da dama sun shirya yin wata irin haɗaka mai ƙarfi domin tunkarar zaben da kifar da shugaban kasa Tinubu
- Wannan na zuwa ne yayin da yan Najeriya da dama suke korafi kan tsare-tsaren gwamnati, sai dai Tinubu bai fara zancen takara ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Wasu kungiyoyi da jam'iyyun adawa sun fara shirin zakulo hanyoyin tumbuke Bola Tinubu a 2027.
Ana hasashen jam'iyyun da kungiyoyi za su yi wata irin haɗaka da ba a taba yi ba domin kifar da Bola Tinubu a zaben 2027.
An soma shirin kifar da Tinubu a 2027
Vanguard ta ce dan Majalisar Tarayya, Hon. Ikenga Imo Ugochinyere ya ce sun shirya haɗaka mai ƙarfi domin tunkarar 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hon. Ikenga ya ce jam'iyyun adawa za su yi gagarumar haɗaka ko da jam'iyyar PDP ko babu ita domin samun nasara a zaben.
Ugochinyere ya ce PDP ta gaza samar da adawa mai karfi a daidai lokacin da kasar ke fuskantar barazana.
Dan Majalisar ya soki gwamnonin PDP kan nuna goyon bayansu ga shugaban jam'iyyar, Umar Damagum.
Ya zarge su da yi wa Ministan Abuja, Nyesom Wike aiki domin ganin PDP ba ta sake tasiri ba a matsayin jam'iyya mai karfi.
Kungiyoyi sun hada kai domin rusa Tinubu
Tsohon kakakin Atiku Abubakar a zaben 2023, Otunba Segun Showunmi ya kaddamar da wata kungiya domin tunkarar Tinubu a zaɓen.
Showunmi ya ce sun sanyawa kungiyar suna National Opposition Movement Coalition (NOMC) domin dawo da martabar dimukraɗiyya.
Har ila yau, kungiyar Coalition of United Political Parties (CUPP) ta goyi bayan tafiyar da ake shirin yi duk da Tinubu bai fara zancen tazarce ba.
PDP ta soki Seyi Tinubu kan harin mulkin Lagos
Kun ji cewa yayin da ake kiran dan shugaba Bola Tinubu mai suna Seyi Tinubu ya tsaya takara, jam'iyyar PDP ta yi martani kan lamarin.
Jam'iyyar hamayyar ta reshen jihar Lagos ta soki masu tunzura Seyi neman takarar gwamnan jihar inda ta ce ba zai yiwu ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng