"Babu Son Zuciya" Sanata Ya Faɗi Abin da Zai Faru da Peter Obi Ya Ci Zaɓen 2023
- Sanata mai wakiltar Abia ta Kudu, Enyinnaya Abaribe ya ce da Peter Obi ya zama shugaban ƙasa a 2023 da yanzu Najeriya ta gyaru
- Abaribe ya ce ɗan takarar Labour Party a 2023 ba zai nuna son zuciya da son rai kamar yadda Bola Tinubi ke nunawa ba
- Ya soki shugaban kasa Tinubu kan naɗa ministoci huɗu daga cikin Ogun, yana mai bayyana hakan da son zuciya ƙarara
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Sanata Enyinnaya Abaribe ya ce da Peter Obi ne ya zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023, da tuni Najeriya ta warke daga ciwon da ya addabe ta.
Sanata Abaribe ya yi ikirarin cewa son zuciyar da ya yi katutu a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ba shi da matsuguni a ƙarƙashin Peter Obi.

Kara karanta wannan
2027: Tinubu Zai Iya Ganin Adawar da Bai Taba Gani ba a Siyasa, Ana Shirin Kifar da Shi

Source: Facebook
Abaribe, sanata mai wakiltar Abia ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya faɗi haka ne a cikin shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels tv yau Litinin.
Abin da Peter Obi zai yiwa Najeriya
Ya yi iƙirarin cewa ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar LP ba zai sa son rai da son zuciya ba idan da ya zama shugaban ƙasa a 2023.
Sanatan ya ce:
“Idan da a ce Peter Obi ya yi nasara a zaɓen da ya wuce, tabbas da kun ga mafi kyawun Najeriya fiye da abin da muke gani a yau.
"Na farko dai ba zai zama mai son zuciya ba kamar wannan gwamnatin, ba zai yi haka ba domin ba haka halinsa yake ba, haka muke mun fi damuwa da damuwar jama'a."
Sanata Abaribe ya caccaki Bola Tinubu
Abaribe ya kuma soki Shugaban kasa Bola Tinubu bisa nadin ministoci hudu daga jihar Ogun, yana mai bayyana hakan a matsayin son zuciya, in ji rahoton Punch.
Ya kuma kara da cewa bai kamata al'ummar Kudu maso Gabas su jira adalci daga shugabannin Najeriya ba, gara ma su maida hankali waken kawo ma kansu ci gaba.
Ƴan majalisr NNPP sun bukaci sauke Ali Madaki
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan NNPP a majalisar wakilai sun buƙaci cire Hon. Ali Madakin Gini daga matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye.
Jam'iyyar NNPP ta ƙasa ta maye gurbinsa da Hon. Tijjani Jobe, mai wakiltar Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado a majalisar wakilai.
Asali: Legit.ng
