Shugaban PDP na Ƙasa Ya Bukaci INEC Ta Shirya Zaben Cike Gurbin Yan Majalisa 27

Shugaban PDP na Ƙasa Ya Bukaci INEC Ta Shirya Zaben Cike Gurbin Yan Majalisa 27

  • Shugaban PDP na ƙasa ya shiga rigimar sauya sheƙar ƴan majalisar dokokin jihar Ribas na tsagin ministan Abuja, Nyesom Wike
  • Umar Damagum ya ributa takarda a hukumance zuwa INEC, ya bukaci ta shirya zaɓem cike gurbin ƴan majalisu 27
  • Damagum ya ce sauya sheƙar da suka yi watanni shida bayan rantsar da su ta saɓawa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Muƙadashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum ya rubuta takarda zuwa ga hukumar zaɓe ta ƙasa watau INEC kan ƴan majalisar dokokin Ribas 27.

Damagum ya bukaci INEC ta gaggauta shirya zaɓen cike gurbi na ƴan majalisar dokokin Ribas guda 27 waɗanda ke goyon bayan ministan Abuja, Nyesom Wike.

Umar Damagum da Wike.
Shugaban PDP ya Bukaci INEC ta canza zaben yan majalisa 27 na jihar Ribas Hoto: Umar Damagum, Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

Shugaban PDP ya aika saƙo ga INEC

A wasiƙar, Damagum ya ce bisa tanadin kundin tsarin Najeriya, ƴan majalisar sun rasa kujerunsu sakamakon sauya shekar da suka yi daga PDP zuwa APC, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa ya ba PDP sirrin kayar da Tinubu a 2027

Idan ba ku manta ba ana zargin ƴan majalisa 27 masu goyon bayan tsagin Wike a rikicin siyasar Ribas sun sauya sheka zuwa APC a watan Disamba, 2023.

Lamarin dai ya jawo surutu nusamman daga ɓangaren Gwamna Siminalayi Fubara, wanda ke gani ƴan majalisun sun rasa kujerunsu.

Damagum ya kafa hujja da kundin tsarin mulki

Damagum ya ce jam'iyyar PDP ta tsayar da ƴan takara 32 a dukkan mazaɓun ƴan majalisar dokokin Ribas a zaɓen 2023 kuma ta samu nasarar lashe kujerun gaba ɗaya.

"Watanni shida bayan rantsar da su, 27 daga cikin ƴan majalisar suka koma APC wanda ya saɓawa sashi na 109(1)(g) na kundin tsarin mulki da ya haramta sauya sheƙa ba tare da dalili ba."

Shugaban PDP ta yabawa hukumar INEC

A ƙarshe shugaban PDP ya karkare da kira ga INEC ta sauke nauyin da ke kanta ta hanyar shirya zaɓen cike gurbi a mazabun waɗannan ƴan majalisa 27.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun taso shugaban PDP na ƙasa da NWC a gaba kan Taron NEC

Damagum ya nuna jin dadinsa kan yadda INEC ta himmatu wajen gina adimokaradiyya a Najeriya, ya kuma bukaci ta yi abin da ya dace.

Damgum ya kara samun goyon baya a PDP

A wani rahoton, kun ji cewa Umar Damagum ya kara samun goyon bayan ci gaba da zama a kujerar shugabancin jam'iyyar PDP ta ƙasa.

Shugabannin PDP na jihohi 36 sun jaddada goyon bayansu ga Damagum a wani taro da suka yi a hedkwatar jam'iyyar da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262