'Ya Manta Asalinsa': Dan Majalisar LP Ya Shan Suka Saboda Sanya 'Hular Tinubu'

'Ya Manta Asalinsa': Dan Majalisar LP Ya Shan Suka Saboda Sanya 'Hular Tinubu'

  • 'Yan soshiyal midiya musamman magoya bayan jam'iyyar LP sun dura kan wani dan majalisar wakilai, Hon. Thaddeus Attah
  • Hon. Attah na fuskantar caccaka daga matasan LP biyo bayan ganin hotonsa da aka yi sanye da 'hula mai tambarin Bola Tinubu'
  • Da yawa daga cikin masu sukar na zargin dan majalisar da juyawa LP baya alhalin ita ce ta kai shi inda yake ba APC ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Wani hoto da ke nuna Thaddeus Attah, ɗan majalisar wakilai, ya jawo ce-ce-ku-ce da tattaunawa mai zafi a dandalin sada zumunta.

A cikin hoton, an ga Hon. Attah, wanda aka zaɓe shi a karkashin jam'iyyar Labour a mazaɓar Eti Osa sanye da hula mai tambarin Shugaba Bola Tinubu na jam’iyyar APC.

"Yan soshiyal midiya sun dura kan dan majalisar wakilai kan sanya hular Tinubu
Dan majalisar wakilai ya taro rigima da 'yan Labour bayan sanya hular Tinubu. Hoto: @_JtAtta
Asali: Twitter

'Dan majalisar LP ya sanya hular Bola Tinubu

Kara karanta wannan

'Ku ja jari': Abokin hamayyar Tinubu a zaben 2023 ya ba matasa 25 kyautar N7.5m

'Dan majalisar ya wallafa hotunan a shafinsa na X, inda masu amfani da dandalin suka yi masa ca game da sanya hular Tinubu alhalin yana jam'iyyar adawa ta LP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin da ya wallafa hotonsa sanye da hula mai tambarin Tinubu, dan majalisar ya ce:

"Ina mai farin cikin yin aiki da kwamitin harkokin kasashen waje a majalisar wakilai ta tarayya yayin da muka zage damtse domin ci gaban Najeriya a kasashen waje.
"Ni da sauran 'yan kwamitinmu, mun ziyarci kasashe daban daban, aikinmu shi ne karfafa dangantakarmu da wadannan kasashe, kuma mun gana da manyan mahukunta."

'Yan soshiyal midiya sun caccaki dan majalisa

Masu amfani da dandalin X su zargi Hon. Attah da komawa goyon bayan BAT (Bola Ahmed Tinubu), inda wasu daga ciki suka rika yi masa tambayoyi kan dalilin saka hular.

@KNaikky:

"@_JtAtta, dan uwa, yanzu da ka sanya wannan hular ta Tinubu, kana so ka fada mana cewa za ka sauya shekara zuwa @OfficialAPCNg? ne"

Kara karanta wannan

Yan majalisa za su gwabza kan bukatar Tinubu na cin bashin $2.2bn

@MichaelOkoroKi1:

"Me ya sa ka sanya hular Tinubu?
"Bai kamata ka yaudari jam'iyyarmu ba."

@uche4luv9576:

"Me ya sa ka sanya hular BAT (Bola Ahmed Tinubu)? Lallai dan siyasa ba abin yarda ba ne. Kowannensu ta aljihunsa yake yi."

@DebbySimon69:

"Na sha fuskantar cin mutunci daga yan barandan Tinubu saboda kare muradunka Mista Atta Thaddeus.
"Menene kake yi haka? 'Yan Obidients sun kare mutuncinka sun zabe ka, da abin da za ka saka masu kenan?"

@NelsonJosiah8:

"Ba don LP ba da yanzu bai zo inda yake ba, amma har ya manta asalinsa, ya manta cewa duk abin da ya hau sama, wata rana zai dawo kasa."

LP ta karyata goyon bayan Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar Labour ta Peter Obi ta karyata jita jitar da ake yadawa na cewa za ta haɗa kai da Bola Tinubu a zaben shekarar 2023.

Daraktan yada labaran LP, Obiora Ifoh wanda ya karyata wannan jita jita ya ce akwai bukatar wadanda ke yadata su kawo hujjoji ba wai su tsaya suna shaci fadi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.