Sheikh Bello Yabo Ya yi Magana kan Masu Kokarin Raba Abba da Kwankwaso
- Shahararren malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Bello Yabo ya yi magana kan masu neman raba kan jagororin NNPP a Kano
- Sheikh Bello Yabo ya ce masu neman kawo rigima a tsakanin Abba Kabir Yusuf da Rabi'u Musa Kwankwaso ba su kyauta ba
- Shehun Malami, Bello Yabo ya yi magana ne bayan wasu mutane sun yawaita kiran 'Abba tsaya da kafarka' a jihar Kano a kwanakin baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Bello Yabo ya yi magana a kan siyasar Kano.
Malam Bello Yabo ya ce a addini ya kamata mutum ya tsaya da ƙafarsa, ba wai a rika zuga mutane su bijirewa iyayen gidansu a siyasa ba.
Shafin Karatuttukan Malaman Musulunci ne ya wallafa bidiyon Sheikh Bello Yabo yana jawabin a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kowa ya tsaya da ƙafarsa a addini
Sheikh Bello Yabo ya bukaci dukkan al'ummar Musulmi su nemi ilimin addini domin tsayuwa da kafafunsu.
Malamin ya ce duk wanda ba shi da ilimin addini zai iya zamowa kamar kwallo malamai suna jifa da shi.
Yabo: Kiran Abba tsaya da kafarka zalunci ne
Sheikh Bello Yabo ya ce masu kiran Abba tsaya da kafarka a jihar Kano ba su yi adalci ba kuma hakan zalunci ne.
Shehun malamin ya ce kamata ya yi su rika kiran kafin zabe ba sai wani ya taimaki dan siyasa su fara neman raba su bayan zabe ba.
Malam Bello Yabo ya kara da cewa wasu yan siyasar ko kansila ba za su iya ci ba sai ta dalilin iyayen gidansu amma a hakan ake so a raba su.
Komai daga Allah yake inji Bello Yabo
Sheikh Yabo ya ce yawanci masu neman raba yan siyasa da iyayen gidansu suna gani kamar an tare musu wani abu ne.
Sai dai a hakikanin gaskiya, malamin ya ce rabon kowa daga Allah ya ke kuma babu wanda ya isa ya tare arzikin da Allah ya ba wani.
Yan takarar kansila sun koma APC a Kano
A wani labarin, mun ruwaito muku cewa jam'iyyar NNPP ta sake gamuwa da matsala yayin da wasu 'yan takarar kansila suka sauya sheka zuwa APC a jihar Kano.
Karkashin jagorancin Jamilu Isyaku Getso, tsofaffin 'yan takarar sun sanar da komawarsu APC ne ta hannun Sanata Barau Jibrin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng