Shugaban Majalisa Ya ba PDP Sirrin Kayar da Tinubu a 2027

Shugaban Majalisa Ya ba PDP Sirrin Kayar da Tinubu a 2027

  • Shugaban majalisar dokokin jihar Bauchi ya gano hanyar da jam'iyyar PDP za ta bi domin sake dawowa kan mulkin ƙasar nan a 2027
  • Abubakar Suleiman ya bayyana cewa PDP na buƙatar zaman lafiya da haɗin kai domin sake ɗarewa kan madafun ikon ƙasar nan
  • Ya nuna damuwarsa kan yadda wasu ƴaƴan jam'iyyar suke ficewa daga cikinta zuwa sauran wasu jam'iyyun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Shugaban majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Suleiman, ya bayyana abin da jam'iyyar PDP ke buƙata domin sake dawowa kan madafun ikon ƙasar nan a 2027.

Shugaban majalisar dokokin ya jaddada cewa zaman lafiya da haɗin kai su ne abin da babbar jam’iyyar adawa ta PDP ke buƙata domin ƙwace mulki a hannun Bola Tinubu.

Shugaban majalisar dokokin Bauchi ya ba PDP shawara
Abubakar Suleiman ya ba PDP shawara kan zaben 2027 Hoto: Abubakar Y. Suleiman
Asali: Facebook

Masu ruwa da tsakin PDP sun yi taro

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun taso shugaban PDP na ƙasa da NWC a gaba kan Taron NEC

Abubakar Suleiman ya bayyana haka ne a garin Misau, a ranar Lahadi, yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP na Bauchi ta Tsakiya, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An shirya taron ne domin tattauna yadda za a ciyar da jam’iyyar gaba tare da taya murna ga tsohon shugaban PDP na jihar, Hamza Koshe Akuyam wanda ya fito daga yankin.

Abubakar Suleiman ya ce samun labarin ƴaƴan PDP na ficewa daga jam'iyyar kodayaushe yana ɓata masa rai.

Shugaban majalisa ya ba PDP shawara

Ya jaddada cewa idan wani mutum ɗaya ko wasu gungun mutane suka bar PDP ko da kuwa baragurbi ne, babban koma baya ne ga ci gaba da wanzuwarta.

Shugaban majalisar dokokin ya yi kira ga dukkanin halastattun ƴaƴan jam’iyyar na jiha da ƙasa baki ɗaya da su haɗa kai domin samun nasarar PDP.

Ya ce dole ne a yi duk abin da zai yiwu domin rage ficewar ƴaƴan jam'iyyar tare da ƙara yawan mambobinta a kowane mataki.

Kara karanta wannan

"Tinubu ne babbar matsalarmu," Tsohon ɗan takarar gwamna ya soki shugaban ƙasa

Gwamnonin PDP sun shawarci Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP ta bayyana damuwarta kan taɓarɓarewar tattalin arziƙin da al’ummar ƙasar nan ke fuskanta sakamakon manufofin gwamnatin Bola Tinubu da APC.

Gwamnonin na PDP sun yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya sake duba manufofinsa kan tattalin arziƙin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng