Hadimin Gwamna Ya Yi Murabus Mai Gidansa na Tsaka da Alhinin Mutuwar Matarsa

Hadimin Gwamna Ya Yi Murabus Mai Gidansa na Tsaka da Alhinin Mutuwar Matarsa

  • Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya rasa hadiminsa na musanman da ya dade yana aiki a gidan gwamnatin jihar
  • Hadiminsa a bangaren wayar da kan al'umma, Aniekeme Finbarr ya yi murabus daga mukaminsa domin neman sauya layi
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake jimamin mutuwar matar gwamnan da aka ake shirin binne ta a cikin wannan mako da muke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Akwa Ibom - Ana jimamin mutuwar matarsa, Gwamna Umo Eno ya sake cin karo da wata matsala a gwamnati.

Hadimin gwamnan a bangaren wayar da kan al'umma, Aniekeme Finbarr ya yi murabus daga mukaminsa.

Hadimin gwamna ya yi murabus daga mukaminsa
Hadimin Gwamna Eno Umo na jihar Akwa Ibom ya yi murabus daga mukaminsa. Hoto: Pastor Umo Eno.
Asali: Twitter

Hadimin Gwamna Eno ya yi murabus

Finbarr ya ajiye aikin ne bayan shafe kusan shekaru goma yana aikin gwamnati kamar yadda ya sanar a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Ba a gama da zargin rigima tsakaninsu ba, Kanin Kwankwaso ya maka Abba a kotu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Finbarr ya rike mukami tun a lokacin gwamnatin Udom Emmanuel kafin Gwamna Eno ya gaje shi.

Dan siyasar ya ce ya yi murabus din ne kawai saboda ya gaji yana so ya sauya layi domin sake kwarewa a wani fannin.

"Bayan shafe kusan shekaru 10 ina aikin gwamnati, na yi tunanin sauya layi domin kwarewa a wani bangare."

- Aniekeme Finbarr

Gudunmawar Finbarr a tsohuwar gwamnati

Finbarr ya rike muƙamin hadimi na musamman a bangaren sadarwa a gwamnatin Udom Emmanuel da ta shude.

Daga bisani, Gwamna Eno ya gaje shi inda ya mayar da shi hadiminsa a bangaren wayar da kan al'umma.

Dan jaridar a cikin sanarwar da ya fitar bai ba da cikakken bayani ba kawai ya ce yana son komawa wani layi ne.

PDP ta sake dage taron NEC a Najeriya

Kun ji cewa jam'iyyar PDP ta sake ɗage taron kwamitin zartarwa na ƙasa watau NEC wanda ta tsara gudanarwa ranar 28 ga watan Nuwamba, 2024.

Kara karanta wannan

Ana zargin alaka ta yi tsami tsakanin Namadi da Badaru, Gwamna ya magantu

Sakataren PDP na ƙasa, Samuel Anyanwu ya ce kwamitin gudanarwa NWC ya yanke shawarar ɗaga taron ne saboda jana'izar matar gwamnan Akwa Ibom.

Anyanwu ya bayyana cewa nan ba da daɗewa ba za a sanar da ranar taron karo na 99 a tarihin jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.