Jam'iyyar Peter Obi Ta yi Magana kan Zargin Goyon Bayan Tinubu a 2027
- A yammacin yau aka samu ikirarin cewa jam'iyyar LP ta Peter Obi za ta yi haɗaka da Bola Tinubu a zaben shekarar 2027 mai zuwa
- Kakakin jam'iyyar ya bayyana cewa babu gaskiya a cikin zancen kuma suna shirin karɓar mulki daga hannun APC ne a 2027
- Obiora Ifoh ya ce duk wanda ya yi zargin za su goyi bayan Bola Tinubu a 2027 ya kamata ya kawo hujjoji domin gamsar da yan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jam'iyyar LP ta yi magana kan raɗe radin haɗaka da shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027.
Daraktan yada labaran LP, Obiora Ifoh ya ce babu gaskiya a cikin zancen cewa za su mara baya ga Bola Tinubu a 2027.
Jaridar Punch ta wallafa cewa lauya mai rajin kare hakkin dan Adam, Adeyanju Deji ne ya wallafa zargin hadakar LP da Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin hadakar Tinubu da LP a 2027
Jam'iyyar Labour mai adawa a Najeriya ta nesanta kanta da zancen cewa za ta goyi bayan shugaba Bola Tinubu a 2027.
Daraktan yada labaran jam'iyyar, Obiora Ifoh ya ce tun zaben 2023 babu wata jam'iyyar adawa mai karfi kamar LP a Najeriya.
Vanguard ta wallafa cewa Ifoh ya kara da cewa zargin da aka musu ya riga ya yadu a duniya kuma ya bata sunan jam'iyyar.
"Dukkan abin da aka fada ba gaskiya ba ne. Mun bayyana cewa bamu da niyyar haɗaka da jam'iyya mai mulki a Najeriya.
Muna kalubalantar Adeyanju Deji da masu tunani irin nasa da su kawo dalili a kan inda muka ce za mu yi haɗaka da Tinubu ko APC a 2027.
Muna kira ga Adeyanju Deji ya daina irin kalaman nan domin suna zubar mana da kimar jam'iyya."
- Obiora Ifoh
Jam'iyyar LP ta bukaci Deji Adeyanju ya bata hakuri tare da miliyoyin magoya bayanta kan zargin da ya yi.
LP ta fara shirin kifar da Tinubu a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar LP ta horas da matasa domin tunkarar babban zaben shugaban kasa na 2027.
Jam'iyyar ta bukaci matasan da kasa yi wa horo su fara shirin shiga Aso Villa bayan zaben 2027 domin za su kori APC daga mulki.
Asali: Legit.ng