Tinubu Zai Gamu da Barazana, Kungiyar Shekarau Ta Yunkuro domin Dawo da Mulki Arewa
- Kungiyar tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ta dage wajen harhado kawunan manyan shiyyar Arewa
- A zaman da kungiyar mai suna 'League of Northern Democrats', ta yi da takwararta ta ACF, ta ce dole a duba matsalolin Arewa
- Sanata Ibrahim Shekarau ya fadi yadda LND ta tattauna da jiga jigan kungiyoyi a shiyyar Arewacin kasar gabanin zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Sabuwar kungiyar tafiyar siyasa a Arewa ta League of Northern Democrats (LND) ta fara motsa shiyyar gabanin zaben shugaban kasa a 2027.
Kungiyar karkashin jagorancin tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ta tuntubi shugabanni a Arewa, ciki har da manyan kungiyoyin kare muradun shiyyar.
Jaridar The Guardian ta wallafa LND ta tuntubi kungiyoyin ACF, da kungiyar dattawan Arewa ta NEF da takwararsu ta ‘Middle Belt Forum’.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar Shekarau ta fara shirin zaben 2027
Nigerian Tribune ta tattaro cewa kungiyar LND ta na son shugabancin Najeriya ya dawo Arewacin kasar nan bayan zaben 2027 da ke tunkarowa.
Ibrahim Shekarau ya tabbatar da cewa sun gana da kungiyoyin Arewa da dama domin samar da hadaka da za ta jagoranci warware matsalolin yankin.
LND: 'Yan Shekarau na tattaro 'yan Arewa
Tsohon Ministan harkokin sufuri, Ibrahim Isa Bio, guda daga cikin yan kungiyar LND da Shekarau ke jagoranta ya yi bayanin manufar harhado kawunan Arewa a halin yanzu.
Ibrahim Isa Bio ya ce;
“ Hadaka ce ta inganta Arewacin Najeriya a nan gaba, domin dawo da kambunta na cigaba da al’ada da shugabanci."
Ziyarar da Kungiyar LND ta kai wa ACF na zuwa ne awanni kadan bayan shugabanta da aka dakatar a yanzu ya yi tir da yadda manufofin Tinubu ke kara jefa jama’a a cikin kangin rayuwa.
Shekarau ya jagoranci sake fasalin siyasar Arewa
A baya mun wallafa cewa tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau ya kafa wata kungiyar rajin farfado da darajar Arewacin Najeriya a siyasar kasar nan gabanin 2027.
Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa jiga-jigan shiyyar Arewa za su tattaru wuri guda domin tattauna hanyar samar da mafita daga yanayin da jama'a ke ciki a siyasance.
Asali: Legit.ng