Majalisa Ta Yi Hukunci kan Maida Wa'adin Shugaban Kasa da Gwamnoni Shekara 6
- Majalisar wakilan kasar nan ta ki amincewa da kudurin da zai mayar da wa'adin shugaban kasa zuwa shekara shida
- Kudurin na nufin zababben shugaban kasa da gwamna da shugabannin kananan hukumomi za su yi mulki sau daya
- Dan majalisa daga jihar Imo, Ikeagwuonu Ugochinyere da wasu yan majalisu 33 ne su ka bijiro da kudurin don samar da daidaito
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Majalisar wakilan Najeriya ta fitar da matsaya kan kudurin da ke neman a kara wa’adin shugaban kasa da gwamnoni zuwa shekaru shida amma wa’adi daya kawai.
A zaman da majalisar ta yi a ranar Alhamis, ta yi fatali da kudurin a neman sake karatu na biyu na sake fasalta tsarin wa’adin mulkin Najeriya.
Jaridar The Cable ta wallafa cewa tun da fari, dan majalisa daga jihar Imo, Ikeagwuonu Ugochinyere da wasu yan majalisu 33 ne su ka bijiro da kudurin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me kudurin rage wa’adin mulki ya kunsa?
Nigerian Tribune ta wallafa cewa kudurin kara wa’adin mulki na son kowane shugaban kasa, gwamna da shugaban karamar hukuma ya rika wa’adi daya na shekara shida kawai.
Haka kuma ana son a samar da ofishin mataimakin shugaban kasa guda biyu, wanda zai wakilci Arewaci da Kudancin Najeriya domin daidaita wakilcin shiyyoyi.
Majalisa ba ta amince da rage wa’adin mulki ba
A yau ne shugaban majalisa, Hon. Tajudeen Abbas ya bukaci wakilan kasar nan da su bayyana ra’ayinsu kan sake duba kudirin a karo na biyu.
A kuri’ar murya da aka kira a zaman na Alhamis, yan majalisar da su ka ce a’a sun shafe muryar wadanda ke bukatar a cigaba da duba kudirin.
Wannan na nufin an yi fatali da neman kara wa’adin zababbun shugabannin siyasa a kasar nan, kamar yadda aka yi a baya.
Majalisa ta nemi rage wa'adin mulki
A wani labarin kun ji cewa majalisar kasar nan ta nemi a rage wa'adin mulkin shugaban kasa, gwamnoni da zababbun shugabannin kananan hukumomi zuwa wa'adi daya.
Amma kudurin ya nemi zababbun shugabannin su shafe shekara shida a wannan wa'adi, sannan a karfafa tsarin karba-karba a tsakanin shiyyoyin kasar nan don kowa ya samu.
Asali: Legit.ng