"Tinubu ne Babbar Matsalarmu," Tsohon Ɗan Takarar Gwamna Ya Soki Shugaban Ƙasa
- Tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Ogun, Segun Sowunmi ya ɗora laifin rikicin da ke faruwa a PDP kan shugaban ƙasa, Bola Tinubu
- Sowunmi ya ce bai ga dalilin da Tinubu zai ɗauki tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike ya naɗa shi minista ba tare da tuntuɓar PDP ba
- Jigon babbar jam'iyyar adawa ya kuma bayyana kwarin guiwar cewa PDP za ta farfaɗo kuma ta koma kan madafun iko a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Wani babban jigon PDP, Segun Sowunmi a ranar Laraba ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne babbar matsalar jam’iyyar.
Sowunmi ya kuma soki naɗa tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a matsayin ministan babban birnin tarayya Abuja.
Segun Sowunmi, tsohon dan takarar gwamnan jihar Ogun a inuwar PDP, ya bayyana haka ne a gidan talabijin na Channels a cikin shirin siyasa a yau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Bola Tinubu ne babbar matsalar PDP'
Ya ce babu dalilin da Shugaba Tinubu zai ɗauki Wike ya ba shi muƙami a majalisar zartaswa ba tare da neman izinin jam'iyyar PDP ba.
Da aka tambaye shi ko menene babbar matsalar da ta hana PDP zaman lafiya, Sowunmi ya ce:
"Mutane da yawa na cewa Wike, ni a gani na shugaban ƙasa, Bola Tinubu ne matsalarmu, ba dalilin da zai ɗauki ɗan cikinmu ya ba shi minista ba tare da ya tuntuɓe mu ba."
Jigon PDP ya soki shugaban kasa Tinubu
Sowunmi ya bayyana cewa lokacin da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya so kafa gwamnatin hadin kan kasa, sai da ya tuntubi dattawan jam’iyyar.
Ya ce idan har Tinubu na son PDP ta zauna lafiya to ya dawo mana da Wike tsagin adawa, kamar yadda The Cable ta rahoto.
PDP za ta magance matsalolinta
Duk da rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar, Sowunmi ya yi imanin cewa PDP za ta shawo kansu ta warwarw komai, kuma ta sake komawa kan karagar mulki.
Ya ce babbar jam’iyyar adawa ba ta mutu kuma lafiyarta ƙalau, yana mai ƙarawa da cewa PDP na kokawa ne don tabbatar dimokradiyya.
PDP ta dakatar da shugabanta na Kuros Riba?
A wani rahoton, kun ji cewa kwamitin gudanarwa NWC na PDP ta kasa ya yi fatali da yunkurin dakatar da shugaban jam'iyyar na jihar Kuros Riba.
Kakakin PDP na ƙasa, Debo Ologunagba ya ce a tanadin kundin tsarin mulki, kwamitin gudanarwa na jiha ba shi hurumin dakatar da shugaba.
Asali: Legit.ng