2027: LP Ta Sha Damara, Ta Samu Dabarar Korar Tinubu daga Shugabancin Najeriya
- Jam'iyyar LP za ta yi amfani da matasa wajen ganin ta samu nasarar darewa kujerar shugaban Najeriya
- Darakta Janar na hadin kan jam'iyyar, Marcel Ngogbehei ya ce za su horar da matasa dabarun da su ka dace
- Ya bayyana dalilin da ya sa LP ke son hawa mulkin Najeriya, inda ya danganta hakan da bukatar ceto yan kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Jam’iyyar LP ta sha alwashin darewa kujerar shugaban kasar Najeriya a kakar zabe ta 2027 mai tunkarowa.
Darakta Janar da ke da alhakin motsa jam’iyya da hada kan ‘ya’yanta, Marcel Ngogbehei ne ya bayyana haka ga matasan jam’iyyar da ya tattauna da su.
Jaridar Guardian ta wallafa cewa LP ta ce ta samu dabarar da za ta taimaka wajen tabbatar mata da nasarar samun kujerar shugaban kasa a 2027 mai zuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
LP na shirin samun nasara a zaben 2027
Jam’iyyar LP ta ce za ta zage damtse wajen neman hadin kan masu ruwa da tsaki gabanin gudanar da zaben shugaban kasa a kakar zabe ta gaba.
Darakta Janar kan hadin kai a jam’iyyar, Marcel Ngogbehei ya nanata muhimmancin tafiya tare da wadanda su ka dace domin kwace kujerar daga shugaba Tinubu.
Dalilin LP na neman shugaban kasa
Jam’iyyar adawa ta LP da ta sha kaye a zaben 2023 ta bayyana cewa za ta sake neman kujerar shugaban kasa ne saboda ceto yan Najeriya daga wahala da su ke sha.
“Kasar nan na wani mataki mai muhimmanci, kuma rawar da za ku taka a matsayinku na matasa ya na da muhimmanci ainun. Ba wai manyan gobe ne ku kawai ba, ku ne karfin tafiyar a yau.”
Ya ce za su hada kai da matasa ta hanyar ba su horo da sauran dabarun tabbatar da hadin kai domin fatattakar APC daga mulkin Najeriya.
Zaben 2027: LP za ta horar da matasa
A baya mun ruwaito cewa jam'iyyar LP na shirin hada kai da jam'iyyun PDP da NNPP domin ganin an samu nasara a kakar zaben 2027, wanda ake sa ran Tinubu zai sake tsayawa takara.
Jam'iyyar PDP ta bakin mataimakin kakakinta na kasa, Ibrahim Abdullahi ya tabbatar da cewa ana cigaba da tattaunawa a kan batun domin gano yadda za a doke APC a kakar zaben gaba.
Asali: Legit.ng