Tinubu Zai Iya Samun Cikas a 2027, Dattawan Arewa Sun Fadi 'Dan Takararsu

Tinubu Zai Iya Samun Cikas a 2027, Dattawan Arewa Sun Fadi 'Dan Takararsu

  • Kungiyar Arewa Consultative Forum ta yanke matsaya kan daga yankin da za ta zabi dan takara a zaɓen shekarar 2027 mai zuwa
  • Shugaban kungiyar ACF, Mamman Mike Osuman ya ce Arewa na fama da tarin matsaloli wanda ba su samun kulawa yadda ya kamata
  • A karkashin haka, shugaban ya ce za su zabi dan Arewa da niyyar kawo dauki ga matsalolin da dama da suka addabi yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Kungiyar Arewa Consultative Forum ta shirya wani taro na musamman a jihar Kaduna.

Shugaban kungiyar, Mamman Mike Osuman ya ce sun shirya taron ne domin nazari kan matsalolin Arewa.

ACF Arewa
Kungiyar ACF ta yi matsaya kan zaben 2027. Hoto: Umaru Dukku
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa Mamman Mike Osuman ya ce ɗan Arewa za su zaba a shekarar 2027.

Kara karanta wannan

'Ba laifinsa ba ne': Kungiyar ACF ta wanke Tinubu, ta fadi masu laifi a matsalolin Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ACF za ta zabi dan Arewa a 2027

Kungiyar Arewa Consultative Forum ta bayyana ra'ayin zaben dan Arewa a babban zaben shekarar 2027.

Daily Post ta wallafa cewa shugaban kungiyar, Mamman Mike Osuman ya ce za su zabi dan Arewa ne domin ya cire musu kitse a wuta.

Shugaban ya yi kira ga yan Arewa kan su zauna cikin shiri domin ceto yankin daga gurbataccen shugabanci a shekarar 2027.

"Akwai bukatar kira na musamman kan sadaukarwa domin ceto al'ummar mu da yankinmu.
Da yawa daga cikin yan uwanmu maza da mata sun nuna son tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.
Saboda haka akwai bukatar mu duba matsalolin yankinmu domin kubutar da mutanenmu daga wahalar rayuwa."

- Shugaban ACF

Mamman Mike Osuman ya ce bayan matsalar tsaro, yankin Arewa bai samun kulawa ta musamman a halin yanzu.

Shugaban ya ce tsare tsaren da gwamnati mai ci ke kawowa za su mayar da yankin Arewa baya sosai.

Kara karanta wannan

'Miyagu sun yi ƙawanya ga Arewa,' ACF ta buƙaci koyar da dabarun kariya

ACF ta yi magana kan tsaro a Arewa

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Arewa Consultative Forum ta nuna damuwa kan yadda rashin tsaro ya yawaita a yankin Arewa.

Shugaban kungiyar, Mamman Mike Osuman ya ce akwai bukatar sake zama domin tunkarar matsalolin Arewa da gaske a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng