'Tinubu na kan Hanya': Sanata Ya Bukaci Obasanjo Ya Rufe Bakinsa, Ya Gargade Shi
- Sanata daga yankin da Olusegun Obasanjo ya fito ya yi masa martani kan sukar gwamnatin Bola Tinubu da yake yi
- Sanata Jimoh Ibrahim ya bukaci Obasanjo ya yi shiru da bakinsa duba da yadda gwamnatin Bola Tinubu ke inganta Najeriya
- Sanatan ya ce kwata-kwata kalaman Obasanjo ba su dace ba a daidai wannan lokaci da ake ciki domin zai kawo rigima
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Yayin da Olusegun Obasanjo yake cigaba da caccakar mulkin Bola Tinubu, sanata ya mayar masa da martani.
Sanata Jimoh Ibrahim ya bukaci Obasanjo ya yi shiru da bakinsa kan shiga lamarin kasar baki daya.

Source: Getty Images
Obasanjo ya soki tsarin mulkin Tinubu
Sanatan da ke wakiltar Ondo ta Kudu ya fadi haka ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a jiya Talata 19 ga watan Nuwambar 2024.

Kara karanta wannan
'Idan babu Arewa, babu Najeriya,' Tinubu ya ce gwamnati za ta bunkasa rayuwar matasa
Wannan martani na zuwa ne bayan Obasanjo ya soki tsarin mulkin Tinubu inda ya ce komai ya tsaya cak a Najeriya.
Olusegun Obasanjo ya kira Bola Tinubu da sunan 'Baba go slow' saboda ikirarin cewa rayuwa ta gagara cigaba a mulkinsa.
Sanata ya mayar da martani ga Obasanjo
Sanatan Jimoh ya ce komai na tafiya yadda ake so a karkashin mulkin Shugaba Tinubu duba da kokarinsa, cewar Vanguard.
"Ina matukar mutunta Olusegun Obasanjo amma kalaman ta da rigima a lokacin zaman lafiya ko kadan ba su dace ba."
"Najeriya tana tafiya yadda ya kamata karkashin wannan mulki na Shugaba Bola Tinubu."
"Mun saɓa da kalaman Obasanjo ba mu tare da shi, bai kamata mutum ya yi amfani da kalaman ta da rigima a wannan lokaci na zaman lafiya ba."
- Sanata Jimoh Ibrahim
Atiku ya yi magana kan rigimarsa da Obasanjo
Kun ji cewa dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar ya fadi wanda ya yi kokarin sulhunta shi da Olusegun Obasanjo.
Atiku ya yabawa halayen tsohon shugaban NDDC, Cif Onyema Ugochukwu kan irin kokarin sulhu da ya yi a tsakaninsa da Obasanjo.
Atiku ya tuno irin dattaku da Ugochukwu ya nuna ba tare da nuna bangare ba inda ya ce tabbas mutum ne mai kishin kasa.
Asali: Legit.ng
