Ifeanyi Ubah: Ndume na Son a Jawo Matar Marigayin Sanata Zuwa Majalisa

Ifeanyi Ubah: Ndume na Son a Jawo Matar Marigayin Sanata Zuwa Majalisa

  • Sanata Ali Ndume ya bukaci majalisa ta marawa matar tsohon takwaransu, marigayi Sanata Ifeanyi Ubah baya
  • Ali Ndume da ke wakiltar Borno ta Kudu na fatan majalisa ta taimakawa matar marigayin domin ta shigo majalisa
  • Ya bayyana cewa matakin zai taimaka wajen tabbatar da dorewar manufofin Ifeanyi Ubah a kan mutanen da ya wakilta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu ya mika bukata ga gaban majalisar dattawan kasar nan kan marigayin dan majalisa, Ifeanyi Ubah.

Sanata Ali Ndume ya bukaci majalisar da ta amince da maye gurbin marigayi Sanata Ifeanyi Ubah da mai dakinsa, Uchenna Ifeanyi Ubah.

Ndume
Ali Ndume ya nemi goyon baya kan shigo da matar marigayi Uba majalisa Hoto: Bukola Saraki/Aliu Haidar Zaifada
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Sanata Ifeanyi Ubah, wanda dan asalin jihar Anambra ne ya rasu a watan Yuli ya na da shekaru 52.

Kara karanta wannan

Shettima ya fadi abin kirki da Marigayi Sanata Ubah ya yi wa Borno lokacin Boko Haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Ndume ya yi ta’aziyyar Ifeanyi Uba

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa Sanatan Borno Ali Ndume ya jajanta da rasuwan takwaransa da ya shafe lokaci a majalisa.

Ya bukaci majalisa ta marawa matar marigayin ya bari baya domin ta dora a kan ayyukan mijinta na cigaban al’umarsa.

“Matan shugabanni na maye gurbin mazajensu,” Ndume

Dan majalisar dattawan, Ali Ndume ya bayyana cewa an sha samun matan Sanatoci, masu rai ko wadanda su ka rasu na maye gurabensu a majalisa bayan sun bari.

A cewar Ndume:

“Wannan ya faru a da a lokacin Chuba Okadigbo, bayan ya rasu matarsa Margery ta shiga majalisa domin cigaba da ayyukansa."

Ali Ndume ya kuma buga misali da matar shugaban kasa, Remi Tinubu wacce ta shiga majalisa bisa ayyukan mijinta a lokacin da ya na gwamnan Legas.

Tinubu: Sanata Ndume na tattaro kan majalisa

A wani labarin mun ruwaito cewa tsohon bulaliyar majalisa, Sanata Ali Ndume ya fara yunkurin hada kan yan majalisa, musamman wadanda su ka fito daga Arewacin kasar nan.

Wannan wani mataki ne na neman goyon baya domin fatali da bukatar da shugaba Bola Ahmed Tinubu ke shirin aikawa gaban majalisa kan sabuwar dokar haraji kan yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.