Sanata Barau Ya Sake Gigita NNPP a Kano, Wasu 'Yan Takarar Kansila Sun Koma APC

Sanata Barau Ya Sake Gigita NNPP a Kano, Wasu 'Yan Takarar Kansila Sun Koma APC

  • Jam'iyyar NNPP ta sake gamuwa da matsala yayin da wasu 'yan takarar kansila suka sauya sheka zuwa APC a jihar Kano
  • Karkashin jagorancin Jamilu Isyaku Getso, 'yan takarar sun sanar da komawarsu APC ne ta hannun Sanata Barau Jibrin
  • 'Yan takarar sun shaidawa Barau cewa sun sauya shekar ne saboda rashin adalcin da shugabannin NNPP suka yi musu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wasu 'yan takarar kujerar kansila daga karamar hukumar Gwarzo, jihar Kano sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a kasa.

Sanata Barau Ibarahim Jibrin, mataimakin shugaban majalisar dattawa ne ya sanar da ficewar 'yan takarar kansilar daga NNPP zuwa APC.

Sanata Barau ya yi magana yayin da wasu 'yan takarar kansilar Kano suka koma APC
'Yan takarar kansila a Kano sun sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC. Hoto: @barauijibrin
Asali: Twitter

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a daren ranar Litinin, Sanata Barau ya ce 'yan takarar kansilar sun sauya sheka saboda rashin adalcin NNPP.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 4 ƴan gida ɗaya a Arewa, suna neman N30m

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan takarar kansila sun bar NNPP a Kano

A cewar mataimakin shugaban majalisar dattawan:

"A yau, na karbi ’yan takarar kansila na karamar hukumar Gwarzo ta Jihar Kano a karkashin jam’iyyar NNPP, wadanda suka sauya sheka zuwa APC.
"Sun tabbatar da cewa matakin da suka dauka na jefar da jar hula ya samo asali ne daga rashin adalci da shugabannin jam’iyyar NNPP suka yi musu."

A karkashin jagorancin Jamilu Isyaku Getso, tawagar ta jefar da jajayen hula, inda suka nuna nadamar kasancewa tare da NNPP.

Barau ya karbi 'yan NNPP zuwa APC

Sanata Barau ya taya 'yan takarar kansilar murnar wannan hukunci da suka yanke tare da yi masu maraba da zuwa jam'iyyar APC, "mafi girman jam'iyyar siyasa a Afrika."

Ya kuma karfafa masu gwiwar yin riko da hadin kai da kuma shiga harkokin APC yana mai cewa wannan matakin zai bunkasa kasa da jam'iyyar baki daya.

Kara karanta wannan

'Ana shirin bautar da mu,' Kwankwaso ya gano makircin da Legas ke kullawa Arewa

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya nuna babbar rawar da matasa ke takawa wajen ci gaban al'umma da kuma amfanin ginansu kan tafiyar da shugabanci.

Kalli hotunan a nan kasa:

'Yan Kwankwasiyya sun koma APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu kusoshin NNPP daga kananan hukumomin Kunchi da Makoda na jihar Kano, sun koma jam’iyyarsu ta asali, watau APC.

Sanata Barau Jibrin, wanda ya karbi masu sauya shekar zuwa APC ya ce 'yan siyasar sun dauki matakin ne saboda rashin adalcin da ake yi a NNPP.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.