Zaɓen Ondo: Jerin Manyan Waɗanda Suka yi Nasara da Waɗanda Suka Tafka Asara

Zaɓen Ondo: Jerin Manyan Waɗanda Suka yi Nasara da Waɗanda Suka Tafka Asara

An kammala zaben Ondo yayin da hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar da cewa gwamna Lucky Aiyedatiwa na APC ne ya lashe kujerar gwamna.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ondo - An kammala zaɓen gwamnan jihar Ondo yayin da dan takarar APC, gwamna Lucky Aiyedatiwa ya samu nasara.

Jam'iyyar APC mai mulki ce ta lashe zaben a dukkan kananan hukumomin 18 na jihar kamar yadda hukumar INEC ta sanar.

Ganduje
Halin da yan siyasa suka shiga bayan zaben Ondo. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje|Official PDP
Asali: Facebook

A wannan rahoton, mun tatttaro muku jerin mutanen da suka tafka babbar asarar da kuma samun nasara a sanadiyar zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗanda suka yi nasara a zaben Ondo

1. Lucky Aiyedatiwa

Gwamna Lucky Aiyedatiwa shi ne ya tsaya takara a karkashin jam'iyyar APC inda ya lashe zaben da kuri'u 366,781.

Kara karanta wannan

An kammala zaben Ondo, INEC ta fadi wanda ya yi nasara, an jero kuri'un APC, PDP

Wannan shi ne karon farko da Lucky Aiyedatiwa ya gwada sa'arsa wajen tsayawa takarar gwamna bayan ya gaji kujerar jihar a 2023.

2. Abdullahi Ganduje

Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya sha alwashin cewa APC za ta lashe zabe a dukkan ƙananan hukumomin jihar Edo.

Burin Ganduje ya zamo gaskiya yayin da APC ta lashe zaben a dukkan ƙananan hukumomin Ondo cikin har da inda dan takarar PDP ya fito.

3. Olusegun Obasanjo

Cif Olusegun Obasanjo ya kasance tsohon shugaban kasa daya da ya taka har jihar Ondo ya yi fatan alheri ga Lucky Aiyedatiwa.

Yayin da ya ziyarci Lucky Aiyedatiwa, Obasanjo ya yi fatan Allah ya ba shi nasara tare da fada masa gwagwarmayar da ya yi a 1999.

Waɗanda suka yi asara azaben Ondo

1. Agboola Ajayi

Dan takarar PDP, Agboola Ajayi na cikin waɗanda ake ganin sun tafka babbar asara a zaben Ondo.

Kara karanta wannan

Ondo: Dan takarar PDP ya ga ta kansa, ya fadi kulle kullen da APC ta shirya

Agboola Ajayi ya kasance wanda ake yi wa tsammanin samun kujerar gwamnan Ondo amma sai ya zo na biyu a zaben.

2. Jagororin PDP

Bayan faduwa zabe a jihar Edo a kudancin Najeriya, jam'iyyar PDP ta saka ran maye gurbin Edo da jihar Ondo.

Rashin samun jihar Ondo ya mayar da lissafin PDP baya ta inda jihohin da ta mallaka suka kara raguwa a Najeriya.

3. Iliya Damagun

A cikin zabe da aka yi a jihohin Najeriya guda biyar tun hawan Tinubu mulki, PDP ta samu jiha daya ne kawai, Bayelsa.

Hakan na nuna cewa shugaban PDP, Iliya Damagun bai kafa tarihin da za a tuna da shi ba saboda gaza samun nasara.

Zaben Ondo: Buhari ya taya APC murna

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya gwamna Lucky Aiyedatiwa murnar lashe zaben gwamnan da aka yi ranar Asabar a Ondo.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadi sirrin da zai ba su nasara a zaben Ondo

Muhammadu Buhari ya fadi wasu abubuwa da ya ke so gwamna Lucky Aiyedatiwa ya mayar da hankali a kai bayan kayar da yan takara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng