Barau Jibrin: 'Abin da Ke Shirin Faruwa a Kano sakamakon Sauya Sheƙar Jiga Jigan NNPP'

Barau Jibrin: 'Abin da Ke Shirin Faruwa a Kano sakamakon Sauya Sheƙar Jiga Jigan NNPP'

  • Sanata Barau I. Jibirin ya ce tururuwar da ƴaƴan NNPP ke yi zuwa APC alama ce ta abin da zai faru a Kano a zaɓen 2027
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce babu sauran ɓurɓushin NNPP ta mazaɓarsa watau jihar Kano ta Arewa
  • Barau ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi manyan ƙusoshin NNPP daga gundumar jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ya ƙara nuna alamun shirin APC na karɓe mulkin Kano a babban zaɓen 2027.

Sanata Barau Jibrin ya ce tururuwar da ƴaƴan NNPP ke yi zuwa APC alama ce babba da ke nuna abin da ke shirin faruwa a jihar Kano a zaɓe na gaba.

Sanata Barau Jibrin.
Sanata Barau ya sake nuna shirin da APC ke yi a Kano gabanin 2027 Hoto: @barauijibrin
Asali: Twitter

Barau Jibrin ya karɓi ƴan mazaɓar Kwankwaso

Kara karanta wannan

Durkusar da Arewa: Sabon Ministan Tinubu ya yi wa Kwankwaso martani, ya gargade shi

Barau Jibrin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi masu sauya sheka daga gundumar jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata sanarwa da ya wallafa a shafin X, Barau ya karɓi masu sauya sheka daga gundumar Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf ciki har da tsohon kansila, Yahaya Sa’idu Kwankwaso.

Da yake maraba da sababbin ‘ya’yan APC, Sanata Barau ya tabbatar musu da cewa za a yi musu adalci da daidaito kuma ba za a nuna masu banbanci ba.

"APC na shirin mamaye Kano" - Barau Jibrin

“Ba za a nuna wariya ga kowa ba, APC jam’iyya ce ta kowa, muna ba kowa dama daidai gwargwado. Wanna sauya sheka daga NNPP zuwa APC alama ce ta abin da ke tafe a 2027.
"Babu sauran ɓurɓushin NNPP a Kano ta Arewa, kuma nan ba da daɗewa ba APC za ta share ragowar ƴan NNPP da suka rage a Kano ta Kudu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun buɗewa motar jami'an tsaro wuta, sun kashe mutum 4

"Yanzu ƴan ƙalilan ne suka san NNPP a Kano ta Tsakiya. Za mu yi duk mai yiwuwa wajen kawo ci gaba a Kano da ƙasa baki ɗaya."

- Barau I. Jibrin.

APC ta fara zawarcin ƴan majalisar NNPP

A wani rahoton, kun ji cewa ƙaramin Ministan gidaje da raya birane, Yusuf Abdullahi Ata ya ce APC na kokarin jawo wasu manyan Kwankwasiyya.

Yusuf Abdullahi Ata ya ce ana zawarcin Sanata AbdulRahman Kawu Sumaila, AbdulMumin Jibrin Kofa da Kabiru Alhassan Rurum.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262