Kano: Tsohon Kansilar Mazabar Kwankwaso da Wasu Jiga Jigan NNPP Sun Koma APC
- Tsohon kansilar mazabar Sanata Rabiu Kwankwaso, Yahaya Sa’idu da wasu jiga-jigan NNPP sun sauya sheka zuwa APC
- Hakazalika, an samu wasu kusoshin jam'iyyar PDP daga karamar hukumar Dawakin Kudu sun koma jam'iyyar APC a Kano
- Sanata Barau Jibrin wanda ya karbi wadanda suka sauya shekar ya ce ayyukan alherin da APC ke shimfidawa ne ya jawo su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wani tsohon kansilar mazabar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a karamar hukumar Madobi jihar Kano ya sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC.
An ce tsohon kansilar mai suna Yahaya Sa'idu Kwankwaso da wasu jiga jiga jam'iyyar NNPP ne suka sauya sheka a ranar 16 ga watan Nuwambar 2024.
Kano: Kusoshin NNPP sun sauya sheka
Sanata Barau Jibrin, mataimakin shugaban majalisar dattawa ne ya sanar da hakan a shafinsa na X inda ya ce masu sauya shekar sun shiga APC ta hannunsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce tsohon kansilar da jiga jigan sun je har gidansa inda suka sanar da ficewarsu daga jam'iyyar NNPP.
Sanata Barau ya ce irin ayyukan alkairin da suke shimfidawa a jihar Kano dsa kasa baki daya ne ya ja ra'ayin mutanen suka koma APC, jam'iyya mai karfi a Afirika.
Kano: Jiga jigan PDP sun koma APC
Hon. Abdulhamid Ahmad Diso, tsohon mataimakin kakakin majalisar karamar hukumar Gwale (gundumar Diso) da Hon. Shu’aibu Isa Kubaraci na cikin tagawar.
A bangaren jam'iyyar PDP kuwa, Sanata Barau ya ce Hon. Garba Alhassan Dawaki ya gagoranci wasu tsofaffin kansiloli da 'yan jam'iyyar daga Dawakin Kudu zuwa APC.
Sanata Barau ya ce ya marabci wadanda suka sauya shekar da hannu biyu inda ya ce APC za ta ci gaba da shimfida ayyukan raya kasa a Kano da Najeriya baki daya.
Asali: Legit.ng