Hukumar INEC Ta Ɗaura Kaso 98% na Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Ondo a IReV
- Hukumar zaɓe INEC ta kusa kammala tattara sakamakon kuri'un da aka kaɗa a zaben gwamnan jihar Ondo wanda ya gudana jiya Asabar
- Bayanai sun nuna cewa an ɗora sama da kaso 98% na sakamakon zaɓen a shafin yanar gizo na tattara sakamakon zaɓe watau IReV
- Haka nan a acibiyar tattara sakamako, INEC ta karɓi sakamako daga kananan hukumomi 13 cikin 18, saura guda biyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ondo - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa watau INEC ta kusa kammala ɗora sakamakon zaben gwamnan jihar Ondo a shafin tattara sakamako IReV.
Zuwa ƙarfe 2:37 na daren nan, an ɗora kaso 98.96% na sakamakon zaben da aka kammala a shafin yanar gizo da INEC ta ware don tatttara sakamako watau IReV.
Ondo: INEC ta kusa gama dora sakamako a IReV
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa zuwa yanzu an ɗora sakamakon rumfunan zaɓe 3,892 a shafin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jihar Ondo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya tana da rumfunan zaɓe 3,933 a faɗin kananan hukumomi 18.
Ƴan takara 17 a inuwar jam'iyyun siyasa daban-daban ne suka fafata a zaɓen gwamnan Ondo wanda aka yi ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2024.
Sai dai duk da haka sakamakon da ke fitowa ya nuna fafatawar ta fi zafi tsakanin manyan ƴan takara biyu, Gwamna Lucky Aiyedatiwa na APC da Agboola Ajayi na PDP.
INEC ta karɓi sakamakon kananan humumomi 13
Zuwa yanzu hukumar zaɓe INEC ta karɓi sakamakon zaɓe daga ƙananan hukumomi 13, saura guda biyar kaɗai ya rage.
Gwamna Aiyedatiwa, ɗan takarar gwamna a inuwar APC shi ne a kan gaba da gagarumin rinjaye a sakamakon ƙananan hukumomi 13 da aka bayyana.
Aiyedatiwa ya samu kuri’u 259,851, ya shiga gaban babban abokin hamayyarsa, Agboola Ajayi na PDP, wanda ya samu kuri’u 81,031 kawo yanzu.
Akwai tazarar ƙuri'u 178,820 a tsakanin ƴan takarar biyu yayin da ya rage saura ƙananan hukumomi biyar, rahoton The Nation.
Gwamna Aiyedatiwa ya ce zai karɓi kaddara
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Aiyedatiwa ya yaba da yadda tsarin zaben ke gudana cikin lumana inda ya ce akwai hasashen APC za ta lashe zabe.
Sai dai gwamnan ya ce idan har aka yi zaben cikin gaskiya da adalci zai karbi dukan sakamakon da aka bayyana ko da bai yi nasara ba.
Asali: Legit.ng