Kai Tsaye: Sakamakon Zaben Gwamnan Ondo daga Gundumomi da Kananan Hukumomi
APC ta lashe zaben wata mazaba a Akure Kudu
Hadimin gwamnan jihar Ondo a harkar yada labarai, Ebenezer Adeniyan ya wallafa sakamakon zaben Unit 04, Ward 7 a karamar hukumar Akure ta Kudu:
APC - 73
PDP - 19
ADC - 2
Abbas Mimiko ya lashe rumfar zabensa
Dan takarar gwamna na jam'iyyar ZLP, Abbas Mimiko ya lashe rumfar zaɓensa.
Jaridar The Cable ta rahoto cewa Abbas Mimiko ya samu ƙuri'a 65 a rumfar zaɓen inda ya doke sauran ƴan takarar gwamnna.
Ward 7, PU20, Mona Clinic, Agbogbo Oke, ƙaramar hukumar Ondo ta Yamma
APC: 60
PDP: 30
ZLP: 65
Aiyedatiwa ya lashe rumfar zabensa
Jaridar The Cable ta rahoto cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa kuma ɗan takarar gwamnan APC a zaɓen Ondo ya lashe rumfar zaɓensa.
Igbo ward 4, PU 5, ƙaramar hukumar Ilaje
APC - 128
PDP - 3
APM - 2
ADP - 2
APC ta lashe rumfar zaɓen Olayide Adelami
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa jam'iyyar APC ta lashe zaɓe a rumfar ɗan takararta na mataimakin gwamna, Olayide Adelami.
A rumfar zaɓe ta 16, Igboroko 2, gunduma ta 03, Ahmadiya Grammar School, Iselu, Owo, APC ta samu ƙuri’u 209, inda ta doke jam’iyyar PDP da ƙuri’u 11.
Gunduma ta uku, PU16
APC - 209
PDP - 198