'Mun Kama Yan APC na Sayen Kuri'u a Zaben Ondo,' PDP Ta Jefa Zargi

'Mun Kama Yan APC na Sayen Kuri'u a Zaben Ondo,' PDP Ta Jefa Zargi

  • Mutanen jihar Ondo sun fara kada kuri'a a zaben gwamnan jihar da ke gudana a dukkan kananan hukumomi 18 a yau Asabar
  • Jam'iyyar PDP ta zargi wasu jami'an APC da raba kudi ga al'umma da wasu kayayyaki domin jan hankulan mutane masu kada kuri'a
  • Yayin da kada kuri'a ta fara nisa, hankula sun fara komawa kan yan takarar PDP da APC domin ganin yadda za su ƙare a zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ondo - Hankula sun karkata kan yadda zaben gwamna ke gudana a jihar Ondo musamman wajen sayen kuri'u.

Jam'iyyar adawa ta PDP ta yi zargin cewa yan APC sun fara jan hankulan masu zabe da kudi da wasu kayayyaki.

Zaben Ondo
PDP ta zargi APC da karya doka a zaben Ondo. Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanai kan zargin da PDP ta yi ne a cikin wani sako da jam'iyyar ta wallafa a shafinta na X a safiyar yau Asabar.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadi sirrin da zai ba su nasara a zaben Ondo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ondo: PDP ta zargi APC da sayen kuri'u

Yayin da mutane suka fara kada kuri'u, PDP ta zargi APC da karya doka a zaben gwamna na jihar Ondo.

Jam'iyyar PDP ta yi zargin cewa APC ta fara sayen kuri'u domin shawo hankulan mutanen da suka fito kada kuri'a.

PDP ta yi ikirarin cewa lamarin ya faru ne a karamar hukumar Akoko ta Kudu maso Yammacin jihar Ondo.

"A yanzu haka mun kama jami'an APC sun fara rudan masu zabe wajen raba musu kudi da wasu kayyakki.
Suna aikata haka ne a mazaba ta 8 a Iwara Oka a karamar hukumar Akoko ta Kudu maso Yammacin Ondo."

- Jam'iyyar PDP

Sayen kuri'a: PDP ta yi kira ga EFCC

Bayan fitar da zargin, Jam'iyyar PDP ta bukaci hukuma mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta dauki mataki.

The Guardian ta wallafa cewa PDP ta bukaci rundunar yan sandan Najeriya ta dauki mataki kan zargin da ta yi wa APC.

Kara karanta wannan

Ondo 2024: Yadda ake cakewa mutane kuɗin Kuri'u a kusa da jami'an EFCC

Abubuwa 6 kan masu zabe a Ondo

A wani rahoton, kun ji cewa mutane kimanin miliyan 2 ne ake saka ran za su kada kuri'a a zaben jihar Ondo na 2024.

Tarin masu zaben za su kada kuri'a ne a tsakanin jam'iyyu 17 da suka tsaya takarar gwamnan jihar yayin da hankali ya fi karkata kan APC da PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng