IReV: Yadda Mutum Zai Duba Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Ondo daga Dakinsa
- Hukumar INEC mai zaman kanta, za ta yi bakin kokarinta wajen gudanar da zaben kwarai a Ondo
- Nan da ‘yan awanni kadan mutanen jihar Ondo za su fita domin zaben wanda zai zama gwamnansu
- INEC ta ke da alhakin shirya zabe kuma wannan karo ana nuna sakamakon kuri’un jama’a a IReV
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Ondo - A zaben Edo, hukumar INEC ta yi kokarin ganin ta gyara sunanta da kimarta a idanun duniya da aka yi zaben gwamna.
Duk da an samu ‘yan korafi a zaben da aka yi, hukumar zaben mai zaman kanta za ta so a ga cigaba a zaben gwamnan jihar Ondo.
An kawo IRev domin gyara zaben Najeriya
A rahoton nan na musamman da Legit ta kawo, an yi bayanin yadda mutane za su ci moriyar fasahar zamani domin lura da zaben.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
INEC ta fito da shafin IReV wanda ake amfani da shi domin bibiyar sakamakon zabe kai-tsaye a lokacin da jama’a su ka kada kuri’u.
A wani rahoto, hukumar INEC ta yi bayanin sauyin da aka samu a harkar zabe.
Masu sha’awar ganin yadda zaben yake gudana za su iya yin rajista a shafin INEC a yanar gizo, daga nan sun huta da jiran a ba su labari.
Yadda ake amfani da IReV a zabe
1. Masu sha’awara bin zaben gwamnan Ondo da za a yi za su iya ziyartar shafin ta: https://www.inecelectionresults.ng/login
2. Wannan adireshi zai kai mutum zuwa shafin yanar gizo domin yin rajista ko makamancin haka
3. Idan mutum sabon-shiga ne, zai yi rajista ta hanyar gabatar da bayansa.
4. Bayan gabatar da bayanai kamar su jihar asali, akwai wurin da za a shiga domin kutsawa cikin asalin shafin.
5. Daga nan za a turawa mutum lambar sirri a akwatin imel da ya yi amfani da shi.
6. Idan mutum ya bude sakon a imel dinsa, zai tabbatar da rajistar da ya yi a shafin sakamakon zabe na INEC.
7. Da zarar an yi wannan, za a tura mutum zuwa inda zai iya ganin kuri’un da aka kada.
8. Mutum zai iya zaben rumfar da yake son ganin sakamakon zabe bayan an tattara kuri’u.
9. Akwai damar ganin kowane irin zabe tun daga na shugaban kasa, majalisa zuwa jihohi.
IReV da sakamakon zaben 2023
An yi ta samun surutu a zaben shugaban kasa da aka yi a 2023 saboda yadda aka samu tangarda wajen wallafa sakamako a kan IReV.
Magoya bayan jam’iyyun adawa sun zargi INEC da magudi, hukumar zabe ta ce tangarda aka samu da ta hana a bibiya zaben kai-tsaye.
Asali: Legit.ng