NNPP Ta Sake Rikicewa a Kano, Dandazon Ƴan Kwankwasiyya Sun Sauya Sheka zuwa APC
- Sanata Barau Jibrin ya sanar da dawowar wasu 'yan jam'iyyar NNPP zuwa APC yana kara jaddada karfin jam'iyyar a Kano
- Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce tawagar ta nuna da na sani na shiga jam'iyyar NNPP makonnin baya
- Hakazalika, wasu shugabannin NNPP daga matakin karamar hukumar zuwa gunduma, sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Makonni bayan shiga NNPP, wasu 'yan jam'iyyar APC daga karamar hukumar Kunchi, jihar Kano, sun koma jam’iyyarsu ta asali.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I Jibrin ya ce dandazon mutane sun ziyarci gidansa tare da sake mubayi'a ga APC.
Dandazon 'yan NNPP sun koma jam'iyyar APC
A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X, Sanata Barau Jibrin ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Sun ziyarci gidana, suna masu bayyana nadamarsu na shiga NNPP, jam’iyya da ke da tasiri a wasu 'yan yankuna na mazabar Kano ta tsakiya."
A cewar sanarwar Sanata Barau, gungun mutanen sun samu shiga NNPP ne ta hannun shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Alhaji Hashimu Dungurawa.
Sai dai kuma, a ranar Alhamis, 14 ga watan Nuwamba, mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce:
"A yau, karkashin jagorancin Auwalu Kasuwar Kuka da Shamsu Susa, sun sanar da dawowarsu jam'iyyar APC, inda suka jefar da jar hular NNPP. "
Shugabannin NNPP sun koma APC
A hannu daya kuma, Sanata Barau ya ce ya karbi bakuncin wasu shugabannin kungiyar nemawa NNPP kuri'u daga matakin tushe, wadanda suka koma APC.
Sauran wadanda suka koma APC sun hada da tsofaffin kansiloli, shugabannin matasa, jami'an kananan hukumomi da na gundumomi na jam'iyyar NNPP.
Sanata Barau ya ce:
"Shugabannin kungiyar masu nemawa NNPP kuri'u na karamar hukumar Makoda, ciki har da Alhaji Gambo Ibrahim Satame, sun koma APC a ofishina da ke cikin majalisar tarayya."
Adam Zango ya bi tafiyar Sanata Barau
A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen jarumin masa'antar Kannywood, Adam A. Zango ya ziyarci mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin.
Sanata Barau ya sanar da cewa Adam A Zango ya yi alkawarin ba da duk wata gudunmawa da ake bukata a tafiyar siyasar gidansa yayin da yake kokarin kawo ci gaba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng