Kano: Sabon Ministan Tinubu Ya Fara Zawarcin Jiga Jigan Kwankwasiyya da NNPP
- Karamin Ministan gidaje da raya birane, Yusuf Abdullahi Ata ya ce APC na kokarin jawo wasu manyan Kwankwasiyya
- Yusuf Abdullahi Ata ya ce ana zawarcin Sanata AbdulRahman Kawu Sumaila, AbdulMumin Jibrin Kofa da Kabiru Alhassan Rurum
- Ya kara da cewa bayan wadannan, APC za ta cigaba da neman sauran yan jam'iyyar NNPP da ke zargin an bata masu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Sabon karamin Ministan gidaje da raya karkara, Yusuf Abdullahi Ata ya fara guda daga cikin ayyukan da ya sa gwamnatin Bola Tinubu ta nada shi.
Karamin Ministan ya fara kokarin ribatar rikicin da ya balle a tafiyar Kwankwasiyya na jam'iyyar NNPP a Kano.
BBC Hausa ta wallafa cewa Yusuf Abdullahi Ata ya bayyana shirinsa na gayyato manyan jam'iyyar NNPP na Kano domin shiga APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC na zawarcin yan Kwankwasiyyan Kano
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Yusuf Abdullahi Ata ya ce ya fara kokarin jawo Sanata AbdulRahman Kawu Sumaila zuwa jam'iyya mai mulki ta APC.
Yusuf Abdullahi Ata ya kara da cewa zai kuma yi kokarin dauko dan majalisar wakilai, Kabiru Alhassan Rurum da AbdulMumin Jibrin Kofa zuwa jam'iyyar.
Dalilin APC na neman yan Kwankwasiyya
Jam'iyyar APC ta fara kokarin jawo wasu daga NNPP da tafiyar Kwankwasiyya bayan an samu baraka a tsakanin yan jam'iyyar a Kano.
Sanata AbdulRahman Kawu Sumaila, Hon Kabiru Alhassan Rurum da Aliyu Sani Madakin Gini sun samu matsala da shugabancin jam'iyyar APC da Kwankwasiyya.
Tuni wasu daga cikin manyan yan jam'iyyar su ka bayyana cewa sun fice daga jagorancin kungiyar siyasar da Kwankwaso yake jagoranta.
An samu matsala a Kwankwasiyya
A baya mun ruwaito cewa tafiyar Kwankwasiyya a jam'iyyar NNPP da ke jihar Kano ta samu babbar baraka bayan wasu daga cikin manyanta sun barranta kansu da Kwankwaso.
Tuni Aliyu Sani Madakin Gini da Kabiru Alhassan Rurum su ka yi bankwana da tafiyar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, yayin da Kawu Sumaila ke takun saka da shugabancin Hashimu Dungurawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng