Ondo 2024: Jerin Jihohin da Jam'iyyun APC da PDP ke Mulki Yau a Najeriya
- A ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba za a gudanar da zaben gwamna a jihar Ondo kamar yadda hukumar INEC ta ayyana
- Bisa dukkan alamu, manyan yan takara da za su kara sun fito daga jam'iyyar APC mai mulki a jihar da kuma jam'iyyar PDP mai adawa
- A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin jihohin da jam'iyyun PDP da APC ke rike da su gabanin zaben da za a yi a jihar Ondo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ondo - Manyan jam'iyyun siyasa na cigaba da ƙoƙarin samun jihar Ondo yayin da za a yi zaben gwamna.
A ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana cewa za a yi zaben.
Yayin da shirye shiryen zaben ke shirin kammala, mun tattaro muku jihohin da APC da PDP ke mulki a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jihohin da APC ke mulki a Najeriya
1. Benue
Jam'iyyar APC ce ke rike da mulki a jihar Benue yayin da gwamna Hyacinth Aliya ya kayar da PDP a zaɓen 2023.
Tsohon gwamnan jihar, Samuel Ortom ya kasance dan jam'iyyar PDP bayan barin APC amma jam'iyyarsa ba ta yi nasara a zaben 2023 ba.
A yanzu haka dai ana samun rikicin cikin gida a APC inda aka samu shugabannin jam'iyya har biyu.
2. Borno
A yanzu haka, jam'iyyar APC rike da mulki a jihar Borno karkashin gwamna Babagana Umara Zulum.
Farfesa Babagana Umara Zulum ya fara mulki a jihar Borno ne tun shekarar 2019 kuma zai kammala wa'adi na biyu a 2027.
3. Cross River
Haka zalika APC ke rike da madafun iko a jihar Cross River karkashin gwamna Bassey Otu tun a bara.
Gwamna Bassey Otu ya fara mulki ne a jihar Cross River tun a Mayun 2023 kuma zai kammala a shekarar 2027.
4. Ebonyi
Jihar Ebonyi na cikin jihohin da suke karkashin jam'iyyar APC a tarayyar Najeriya karkashin gwamna Francis Nwifuru.
Gwamna Francis Nwifuru ya fara mulki ne a shekarar 2023 kuma zai kammala wa'adin farko a shekarar 2027.
5. Edo
Jihar Edo tana karkashin jam'iyyar APC karkashin jagorancin gwamna Monday Okpebholo bayan samun nasara a watan Satumba kamar yadda the Cable ta wallafa.
A watan Satumban da ya wuce aka yi zabe kuma dan takarar APC ya kayar da dan PDP duk da cewa gwamnan jihar, Godwin Obaseki dan PDP ne a lokacin zaben.
Ana sa rai Gwamna Monday Okpebholo zai kammala wa'adin mulki na farko ne a shekarar 2028 bayan ya yi shekaru hudu.
6. Ekiti
A yanzu haka, jam'iyyar APC ke mulki a jihar Ekiti karkashin jagorancin gwamna Biodun Oyebanji.
Gwamna Biodun Oyebanji ya fara mulki ne a shekarar 2022 yayin da zai kammala wa'adin farko a 2026.
7. Gombe
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ke rike da madafun iko a jihar Gombe karkashin jami'yyar APC.
Muhammadu Inuwa Yahaya ya fara mulki ne a jam'iyyar APC tun shekarar 2019 kuma zai kammala wa'adi na biyu a 2027.
8. Imo
BBC ta wallafa cewa gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya kasance ƙarƙashin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Mai girma Hope Uzodinma ya fara mulki ne a shekarar 2020 kuma zai kammala wa'adin karshe a shekarar 2028.
9. Jigawa
Gwamna Umar A. Namadi ke jagorantar jihar Jigawa karkashin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Umar Namadi ya gaji ministan tsaron Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar a shekarar 2023.
10. Kaduna
Jihar Kaduna ta kasance ƙarƙashin jam'iyyar APC bisa jagorancin Uba Sani da ya biyo bayan Nasir El-Rufai.
Gwamna Uba Sani ya fara mulki ne a shekarar 2023, ya na sa ran zai shafe akalla shekaru hudu a kujerar mulki.
11. Katsina
Gwamna Dikko Umaru Radda ya fara mulki karkashin APC a shekarar 2023 a jihar Katsina.
A yanzu haka gwamna Dikko Umaru Radda ne shugaban gwamnonin Arewa maso Yammacin Najeriya.
12. Kebbi
Gwamnan jihar Kebbi, Malam Nasir Idris ya samu mulki ne a ƙarƙashin jam'iyyar APC mai ci a Najeriya.
Kamar Katsina, Nasir Idris ya fara mulki ne a APC sakamakon fasa takarar tsohon Minista, Abubakar Malami.
13. Kogi
Ahmed Usman Ododo ke mulkin jihar Kogi a inuwar jam'iyyar APC mai mulki Najeriya bayan doke SDP da sauran jami'yyu.
Alhaji Ahmed Usman Ododo ya karbi mulki ne a shekarar 2024 daga hannun uban gidansa a siyasa watau Yahaya Bello.
14. Kwara
Jihar Kwara ta kasance cikin jihohin Arewa da ke karkashin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Gwamna Abdulrahman Abdularzaq ya fara mulki a jihar Kwara ne a shekarar 2019 kuma zai kammala a 2027.
15. Legas
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ne ke jagorantar mulki a jihar Legas karkashin jam'iyyar APC.
Babajide Sanwo-Olu ya fara mulki a Legas ne tun shekarar 2019 lokacin da aka yi waje da Akinwumi Ambode.
16. Nasarawa
Jihar Nasarawa ta kasance ƙarƙashin mulkin APC bisa jagorancin gwamna Abdullahi Sule.
Gwamna Abdullahi Sule ya fara mulki a 2019 kuma ya samu tazarce duk da an tada masa hankali a kotun zabe.
17. Neja
Gwamna Muhammad Umaru Bago ke jagorantar jihar Neja a karkashin jam'iyyar APC mai mulki.
Gwamna Umaru Muhammad Bago ya fara mulki a shekarar 2023 kuma zai kammala wa'adin farko a shekarar 2027.
18. Ogun
Jihar Ogun ta kasance ƙarƙashin jam'iyyar APC bisa jagorancin gwamna Dapo Abiodun tun shekarar 2019.
Prince Dapo Abiodun mai shekara 64 a duniya ya na cikin gwamnonin APC da suka fi dadewa a ofis a yau.
19. Ondo
Jihar Ondo ta kasance ƙarƙashin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya karkashin gwamna Lucky Aiyedatiwa.
A ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban da muke ciki za a gudanar da zaben gwamna a jihar Ondo.
20. Sokoto
Jihar Sokoto ta kasance ƙarƙashin jam'iyyar APC wanda gwamna Ahmed Aliyu Sokoto ke jagoranta.
Ahmed Aliyu ya gaji Aminu Waziri Tambuwal kuma ya na da goyon bayan Aliyu Magatakarda Wammako.
21. Yobe
Jihar Yobe ta kasance ƙarƙashin APC tun a Mayun shekarar 2019 bisa jagorancin gwamna Mai Mala Buni.
A tarihi jam'iyyar PDP ba ta taba yin mulki a Yobe ba. 'Yan adawa za su jarraba sa'arsu a farkon shekarar 2023.
Jihohin da PDP ke mulki a Najeriya
1. Zamfara
Jihar Zamfara ta kasance ƙarƙashin jam'iyyar PDP bisa jagorancin gwamna Dauda Lawal tun a shekarar da ta wuce.
Gwamna Dauda Lawal ya fara wa'adin farko bayan kayar da gwamnan APC, Bello Matawalle a wani zabe da ya yi zafi.
2. Taraba
Gwamna Agbu Kefas ke jagorantar jihar Taraba a karkashin jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya bayan doke APC, NNPP, LP da sauransu
Gwamna Agbu Kefas ya fara mulki a jihar Taraba ne karkashin PDP a bara da ya canji Darius Ishaku wanda ya shekaru takwas a mulki.
3. Rivers
Jihar Rivers ta kasance ƙarƙashin jam'iyyar PDP bisa jagorancin gwamna Siminalayi Fubara da ya gaji Nyesom Wike.
Gwamna Fubara ya fara mulki a bara kuma zai kammala wa'adi na daya a shekarar 2027 idan ya tsallake rikicin majalisa.
4. Filato
Jihar Filato ta kasance ƙarƙashin jam'iyyar PDP bisa jagorancin Mai girma Caleb Mutfwang da ya fara mulki a 2023.
5. Oyo
Oyo na cikin jihohin yankin Kudu maso Yammacin Najeriya da ke karkashin PDP. Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo zai kammala wa'adi na biyu ne a shekarar 2027.
6. Osun
Duk da karfin APC, jihar Osun ta kasance ƙarƙashin jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya bisa jagorancin gwamna Ademola Adeleke.
7. Enugu
Jihar Enugu ta kasance ƙarƙashin jam'iyyar PDP bisa jagorancin gwamna Peter Mbah da ya fara mulki a shekarar 2023.
8. Delta
Jihar Delta ta kasance ƙarƙashin jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya bisa jagorancin gwamna Sheriff Oborevwori.
9. Bayelsa
Jihar Bayelsa na cikin jihohin da suke karkashin PDP a Kudancin Najeriya bisa jagorancin gwamna Douye Diri.
10. Bauchi
Jihar Bauchi ta kasance ƙarƙashin jagorancin gwamna Bala Abdulkadir Muhammad a PDP wanda ya fara mulki a shekarar 2019.
11. Akwa Ibom
Jihar Akwa Ibom ta kasance ƙarƙashin PDP wanda gwamna Umo Eno ke jagoranta kuma ya fara mulki ne a 2023.
12. Adamawa
Jihar Adamawa ta kasance ƙarƙashin jam'iyyar PDP da gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ke jagoranta.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya fara mulki ne a shekarar 2019 kuma zai kammala a shekarar 2027.
APC ta yi yakin neman zabe a Ondo
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi gagarumin yakin neman zabe a jihar Ondo ranar Laraba.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ne ya jagoranci tawaga mai karfi domin taya gwamna Lucky Aiyedatiwa neman kuri'u.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng