Zaben Ondo: Jerin Gwamnoni da Suka Mulki Jihar daga 1999 Zuwa Yanzu

Zaben Ondo: Jerin Gwamnoni da Suka Mulki Jihar daga 1999 Zuwa Yanzu

  • A ranar Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024 za a gudanar da zaben gwamna a jihar Ondo da ke Kudancin Najeriya
  • Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam'iyyar APC na daga cikin wadanda za su fafata a zaɓen da za a yi domin samun nasara
  • Yayin da ake shirin zaben, Legit Hausa ta duba gwamnoni da suka mulki jihar daga 1999 zuwa shekarar 2024 da muke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - An kirkiri jihar Ondo a watan Fabrairun 1976 daga rusasshiyar yankin Yammacin Najeriya.

Jihar da ake yi wa lakabi da 'Sunshine state' ta samu gwamnoni akalla 19 da suka mulke ta da suka hada da sojoji da kuma na farar hula tun farkon kafa ta.

Gwamnonin da suka mulki jihar Ondo daga 1999 zuwa yau
Jerin gwamnoni da suka jagoranci jihar Ondo daga 1999 zuwa yanzu. Hoto: Dr Olusegun Mimiko, Rotimi Akeredolu Aketi, Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa.
Asali: Facebook

1999-2024: Gwamnoni da suka mulki jihar Ondo

Kara karanta wannan

Zaben Ondo: Ana dab da fara zabe, 'yan daba sun farmaki 'yan PDP

Legit Hausa ta yi bincike da tsamo jerin gwamnoni da suka mulki jihar daga 1999 zuwa yau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Adebayo Adefarati - AD (Mayun 1999 - Mayun 2003)

Adebayo Adefarati shi ne zaɓaɓɓen gwamnan jihar Ondo na farko bayan dawowa siyasa a 1999 karkashin jam'iyyar AD, cewar rahoto a Wikipedia.

Adefarati ya yi wa'adi daya ne kacal a mulkin jihar daga shekarar 1999 zuwa 2003 bayan dawowa mulkin mukraɗiyya.

Wani rahoto na The Nation ta ce Adefarati ya rasu ne yana da shekaru 76 a duniya a ranar 29 ga watan Maris a 2007.

2. Olusegun Agagu - PDP (Mayun 2003 - Fabrairun 2009)

Olusegun Agagu ya karbi mulkin jihar Ondo bayan kayar da Adebayo Adefarati a shekarar 2003.

Agagu ya mulki jihar daga 29 ga watan Mayun 2003 zuwa Fabrairun 2009 inda kotu ta rusa zabensa tare da ba Olusegun Mimiko da ya kasance na biyu a zaben nasara.

Kara karanta wannan

Zaben gwamna: Kashim Shettima ya fadi dalilan da za su sa a kara zaben APC a Ondo

Jaridar Vanguard ta tabbatar da cewa tsohon Ministan ya rasu a shekarar 2013 yana da shekaru 65.

3. Olusegun Mimiko - PDP (Fabrairun 2009 - Fabrairun 2017)

Olusegun Mimiko shi ne gwamna na uku da aka zaba a jihar bayan dawowa dimukraɗiyya a 1999.

Mimiko ya karbi mulki daga shekarar 2009 zuwa 2017 wanda ya shafe shekaru takwas kenan a kan mulki.

Tsohon gwamnan da ya koma jam'iyyar LP kafin sake dawowa PDP shi ne gwamna na farko da ya fara yin nasarar zaɓe a karo na biyu.

4. Rotimi Akeredolu - APC (Fabrairun 2017 - Disambar 2023)

Marigayi tsohon gwamna, Rotimi Akeredolu wanda ya kasance lauya kuma tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta NBA ya karbi mulki daga 2017 kafin rasuwarsa a 2023.

Akeredolu ya rasu yana da shekaru 67 a kasar Jamus da aka ce cutar daji ce ta yi ajalinsa inda aka rantsar da mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa.

Kara karanta wannan

Ondo 2024: Aiyedatiwa da wasu jerin ƴan takarar gwamna 3 da za su iya lashe zabe

5. Lucky Aiyedatiwa - APC (Disambar 2023 - zuwa yanzu)

Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya karbi ragamar mulkin jihar a 2023 bayan rasuwar mai gidansa, Rotimi Akeredolu.

Aiyedatiwa ya rike muƙamin mataimakin gwamna daga 2021 zuwa 2023 karkashin marigayi, Akeredolu.

Gwamna Aiyedatiwa na daga cikin yan takara da za su fafata a zaɓen da za a gudanar a ranar Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024 a kokarin neman zarcewa a karo na

Laifuffuka da za su jefa mutum kurkuku a zaben Ondo

Kun ji cewa dokar hukumar zabe ta shekarar 2022 da ta bayar da gudanar da damar zabukan gwamnoni a wasu jihohin zai tabbata a zaben Ondo.

Dokar ba ta bayar da damar gudanar da zaben a jihohin Bayelsa, Imo, Kogi, Ondo da Edo kawai ba, ta tanadi wadansu matakan hana magudi.

Dukkanin laifuffukan da dokar ta lissafa za su iya jefa mutum a gidan yari na tsawon shekaru, hakan zai danganta da girman laifin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.