'Babu Mai Karya Ni': Wike Ya Fusata kan Rigimar PDP, Ya Soki Gwamna kan Matsalarta

'Babu Mai Karya Ni': Wike Ya Fusata kan Rigimar PDP, Ya Soki Gwamna kan Matsalarta

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike ya caccaki Gwamna Bala Mohammed kan rashin iya shugabanci da zai hada kan yan PDP
  • Wike ya ce abin takaici ne kowa nema yake ya kassara shi inda ya ce ba zai yi tasiri ba wurin shawo matsalolin jam'iyyar
  • Tsohon gwamnan ya ce babu yadda aka iya da shi saboda babu mahalukin da ya isa ya durkusar da shi kamar yadda suke zato

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi magana kan rigimar cikin gidan jam'iyyar PDP a Najeriya.

Tsohon gwamnan Rivers ya ce babu yadda za a shawo kan rigimar idan ana neman durkusar da shi.

Wike ya sha alwashi cigaba da zama gagara-badau a PDP
Nyesom Wike ya soki Gwamna Bala Mohammed ta neman tarwatsa jam'iyyar PDP. Hoto: Nyesom Wike.
Asali: Twitter

'Na zama gagarabadau a PDP' - Nyesom Wike

Wike ya fadi haka ne a birnin Abuja a jiya Laraba 13 ga watan Nuwambar 2024 yayin hira da yan jaridu, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Wike ya sake taso Atiku a gaba, ya fadi makomar takararsa a PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya ce shugabancin jam'iyyar a yanzu shi ne mafi muni a tarihinta duba da yadda aka gaza samar da daidaito.

Ya tabbatar da cewa jam'iyyar ba ta mayar da hankali wurin shawo kan matsalolinta ba yayin da wasu ke neman durkusar da shi.

"Bari in fada muku gaskiya, ba wai PDP ba za ta iya shawo kan matsalolinta ba ne illa wasu suna fifita bukatunsu ne kawai."
"Maganar cewa sai na kai Wike kasa babu abin da zai sauya, kuskure ake tafkawa saboda babu yadda aka iya da ni."

- Nyesom Wike

Wike ya caccaki Gwamna Bala kan rigimar PDP

Wike ya zargi Gwamna Bala Mohammed da tarwatsa PDP yayin da ya gaza hada kan yan jam'iyyar, Daily Post ta ruwaito.

Ya ce babu lokacin da jam'iyyar ta samu mummunan shugabanci irin yanzu musamman shugaban gwamnoni, Bala Mohammed.

Wike: Minista ya tabo zancen takarar Atiku a PDP

Kara karanta wannan

Basarake ya yi magana da ake zarginsa da kiran mambobin PDP su farmaki yan APC

Kun ji cewa Nyesom Ezenwo Wike ya yi magana kan yiwuwar ko Atiku Abubakar zai samu tikitin takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2027.

Ministan na birnin tarayya Abuja ya bayyana cewa babu wata dama da PDP za ta sake ba Atiku domin ya nemi takarar shugabancin Najeriya.

Wike ya yi nuni da cewa lokaci ya yi da za a gwada wani daban domin ƴan Najeriya sun nuna cewa ba za su zaɓi Atiku ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.