Zaben 2027: Wike Ya Sake Taso Atiku a Gaba, Ya Fadi Makomar Takararsa a PDP
- Nyesom Ezenwo Wike ya yi magana kan yiwuwar Atiku Abubakar ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2027
- Ministan na birnin tarayya Abuja ya bayyana cewa babu wata dama da PDP za ta sake ba Atiku domin ya nemi takarar shugabancin kasa
- Wike ya yi nuni da cewa lokaci ya yi da za a gwada wani daban domin ƴan Najeriya sun nuna cewa ba za su zaɓi Atiku ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan yiwuwar Atiku Abubakar ya samu takarar shugaban ƙasa a PDP a shekarar 2027.
Wike ya bayyana cewa Atiku bai da wata dama ta samun tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2027.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a ofishinsa da ke Abuja ranar Laraba, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nyesom Wike ya caccaki Atiku Abubakar
Wike ya kuma yi shaguɓe kan iƙirarin da Atiku ya yi na cewa manufofinsa kan tattalin arziƙi za su ceto Najeriya fiye da na gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Ministan ya bayyana cewa ko a baya Atiku ya taɓa gabatar da manufofin ga ƴan Najeriya, amma ba su zaɓe shi ba, rahoton Vanguard ya tabbatar.
"PDP ba za ta ba Atiku dama ba", Wike
"Shin bai gabatar da shi a gaban ƴan Najeriya ba? Shin ƴan Najeriya sun zaɓe shi? Kawai so yake ya ƙara samun dama, amma wannan damar ba za ta samu ba."
"A wace jam'iyyar? Ta yaya za mu dogara da mutum ɗaya na tsawon shekaru?"
"Ku duba Amurka. Na tabbata da yawa daga cikinku ba su goyi bayan Trump ba saboda maganganun da ake yi a kansa. Amma Amurkawa suna da na su tunanin na daban, kuma sun ɗauki matakin da zai amfani ƙasarsu."
"Ka gabatar da manufufinka a 2023, ƴan Najeriya sun fahimce ka da kyau sannan suka ce mun gode amma ba mu buƙata. Ba za mu goyi bayan ka ba. Sukar gwamnati ba wai shi ne yake nuna ƴan adawa na yin abin da ya dace ba."
- Nyesom Wike
Wike ya faɗi aikinsa a Abuja
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana babban aikin da ya je yi a kujerar da yake kai.
Nyesom Wike ya bayyanawa mazauna birnin cewa babban burinsa shi ne inganta ababen more rayuwa a Abuja maimakon ya riƙa sayar da filaye.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng