Kano: Sanata Kawu Sumaila Ya Sake Kinkimo Rigima a Jam'iyyar NNPP
- Sanata Kawu Sumaila ya yi barazanar kai ƙarar shugaban NNPP, Hashimu Dungurawa gaban kotu kan zargin ƙagen da ya masa
- A wata wasika da lauyan sanatan ya aike wa Hashimu, ya bukaci ya fito bainar jama'a ya janye kalamansa kuma ya ba da hakuri
- Tun farko dai shugaban NNPP ya zargin Sanata Kawu da cinye kudin aikin mazabu da kuma karɓar cin hanci don magudin zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Sanata Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta Kudu ya yi bazaranar maka shugaban NNPP na jihar Kano, Hashimu Dungurawa a kotu kan ɓata masa suna.
Sanata Kawu na jam'iyyar NNPP ya ce ba zai zauna ya zuba ido ana masa kage da ɓata masa suna haka kurum ba.
Kawu Sumaila ya bukaci shugaba NNPP reshen Kano ya janye wannan zargin da ya laƙaba masa cikin sa’o’i 24 ko ya ɗauki matakin shari'a, Tribune Online ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane zargi shugaban NNPP yake yi wa Sumaila?
Hakan na kunshe ne a wata takarda da lauyan sanatan, Sani Musa (SAN) ya aike wa Hashimu Dungurawa kan kalaman da ya yi.
Tun farko dai Hashimu Dungurawa ya zargi Sanata Kawu Sumaila da karkatar da Dala miliyan 80 da aka ba shi na ayyukan mazaɓu.
Wannan dai na zuwa ne a lokacin da rikicin cikin gida ke ƙara ƙamari a jam'iyyar NNPP mai mulkin Kano.
Wasikar lauyoyin Sanata Kawu Sumaila
A wasiƙar, lauyan sanatan sun ce shugaban NNPP ya yi ikirarin Kawu Sumaila ya yi sama da faɗi da kudin aikin ruwan ƙaramar hukumar Sumaila lokacin yana ɗan majisar wakilai.
Haka kuma Hashimu ya ce Sanata Sumaila ya karbi dala miliyan 80 daga hannun Abubakar Kabiru Bichi don yin magudin zaben gwamnan Kano a 2023.
Kawu Sumaila ya ba shugaban NNPP awanni 24
Lauyan Kawu Sumaila ya ce:
"Abokin hulɗarmu ɗan siyasa ne mai nagarta, wanda bai taɓa haɗa hanya da cin hanci da rashawa ko halatta kudin haram ba."
Sanata Kawu Sumaila ya bukaci shugaban NNPP ya fito bainar jama'a janye zargin cikin sa’o’i 24 sannan kuma ya ba shi hakuri kuma a buga labarin a jaridu.
Ɗan NNPP ya goyi bayn harajin Tinubu
A wani rahoton, an ji cewa ɗan majalisar Kano mai wakiltar Kiru/Bebeji, Hon. AbdulMumin Jibrin Kofa ya bayya goyon baya ga sabon kudurin Tinubu.
Ya ce ya na da tabbacin majalisa za ta marawa kudurin haraji da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ke kokarin aikawa masu baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng