Bayan Tsokanar Gwamna, Sanata a Arewa na Fuskantar Kiranye daga Yan Mazabarsa
- Wasu yan mazabar Sanata Shehu Buba da ke wakiltar Bauchi ta Kudu sun fara shirin yi masa kiranye daga Majalisa
- Rahotanni sun tabbatar da cewa yan mazabar suna zargin Sanatan da yaudararsu da kuma zargin asalin tushensa a jihar
- Hakan ya biyo bayan zarge-zargen da ake yi wa Sanata Buba kan alaka da yan ta'adda wanda ya sha musanta hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bauchi - Sanata Shehu Buba ya sake shiga matsala daga yan mazabarsa a jihar Bauchi.
Sanatan da ke wakiltar Bauchi ta Kudu na fuskantar kiranye daga mazabarsa kan zargin alaka da yan ta'adda.
An fara shirin kiranye ga Sanata Buba
A cikin wani rahoto da Legit ta samu, wasu a mazabar sanatan sun fara kokarin yi masa kiranye saboda zarge-zarge.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan har suka cika ka'idar kiranye, hukumar INEC za ta yi kuri'ar raba gardama domin sanin ko ya cancanci Buba ya bar kujerarsa, cewar Blueprint.
"Idan har muka yi nasara, hakan zai zama izina ga sauran yan siyasa da ke ganin za su iya yaudarar al'umma su tsira."
- Cewar wani dan mazabar Sanata Buba
Musabbabin neman yi wa Sanata Buba kiranye
Rahotanni sun tabbatar da cewa abin da ke kara rura wutar shi ne ana kokwanton ko Sanata Shehu Buba dan asalin jihar Bauchi ne.
Wasu na zargin Sanata Buba ya fito ne daga Barikin Ladi da ke jihar Plateau ba Bauchi ba kamar yadda ake zato.
Pulse ta ce Buba ya yi suna a siyasa ne tun bayan rike muƙamin hadimi a gwamnatin Isa Yuguda a jihar Bauchi.
Daga bisani, ya hada tafiya dan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da kuma kungiyar Miyetti Allah a Najeriya.
MURIC ta kare Sanata kan zargin ta'addanci
Kun ji cewa Kungiyar MURIC ta yi Allah wadai da zargin Sanata Shehu Buba da ake yi da ɗaukar nauyin ta'addanci a Najeriya.
Kungiyar kare hakkin Musulmai ta ce babu hujjoji kan zargin sanatan wanda ya kasance haziki da ke hidimtawa al'ummarsa.
Hakan ya biyo bayan zargin da gwamnatin jihar Bauchi ta yi kan sanatan da daukar nauyin dan ta'adda zuwa aikin hajji.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng