Majalisa Ta Dakatar da 'Dan Jam'iyyar PDP, Yan Sanda Sun Fitar da Shi Waje

Majalisa Ta Dakatar da 'Dan Jam'iyyar PDP, Yan Sanda Sun Fitar da Shi Waje

  • Majalisar jihar Delta ta dakatar da mambanta, Hon. Oboror Preyor dan jam'iyyar PDP mai mulki kan nuna rashin da'a
  • An dakatar da dan Majalisar da ke wakiltar mazabar Bomadi a jihar har na tsawon kwanaki 14 kan halayensa da ya nuna
  • Shugaban Majalisar a Delta, Hon. Dennis Guwor shi ya tabbatar da dakatar da Preyor yayin zamanta a yau Laraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Delta - Majalisar dokokin jihar Delta ta sake dakatar da mambanta kan rashin da'a.

Majalisar ta dauki matakin ne kan Hon. Oboror Preyor daga jam'iyyar PDP da ke wakiltar mazabar Bomadi.

Majalisar Delta ta dakatar da mambanta na tsawon makwanni 2
Majalisa jihar Delta ta dakatar da mambanta, Hon. Oboror Preyor. Hoto: Kenneth Oboror Preyor.
Asali: Facebook

An dakatar da dan Majalisar dokokin Delta

The Guardian ta ce an dakatar da Preyor ne a zaman Majalisar a yau Laraba 13 ga watan Nuwambar 2024.

Kara karanta wannan

Rayukan matasa sun salwanta bayan ruftawar mahakar ma'adanai a Filato

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban Majalisar jihar Delta, Hon. Dennis Guwor shi ya tabbatar da matakin da suka ɗauka kan Preyor a yau Laraba.

Dakatarwar ta biyo bayan korafin Hon. Emeka Nwaobi na jam'iyyar PDP daga mazabar Aniocha ta Arewa.

Kafin dakatar da Preyor har na tsawon kwanaki 14, shi ne shugaban kwamitin ayyuka na musamman a Majalisar.

Kakakin Majalisar, Guwor ya ce sun kafa kwamiti na musamman domin yin bincike kan mamban da aka dakatar.

'Dan sanda ya fita da 'dan Majalisa

"Majalisar dokokin Delta ta dakatar da mambanta mai wakiltar mazabar Bomadi kan rashin da'a da ya nuna."
"Nan ba da jimawa ba, za a kafa kwamiti na musamman domin yin bincike kan lamarin."

- Dennis Guwor

Daga bisani, Guwor ya bukaci jami'in dan sanda a Majalisar ya fita da mamban daga harabarta nan take, Vanguard ta ruwaito.

An dakatar da dan majalisar dokokin Delta

Kara karanta wannan

An samu bayanai kan sakon Lakurawa ga Bello Turji game da ayyukan ta'addanci

A baya, mun ba ku labarin cewa Majalisar dokokin jihar Delta ta ɗauki matakin ladabtarwa kan ɗaya daga cikin mambobinta.

Majalisar Delta ta dakatar da mamban da ke wakiltar mazaɓar Ukwuani, Chukudi Dafe, bisa zarginsa da aikata ba daidai ba.

Dakatarwar da aka yi wa ɗan majalisar ya jawo ce-ce-ku-ce saboda ƙin bayyana takamaiman laifin da ake zarginsa da aikatawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.