Jam'iyyar PDP Ta Tono Zargin Yadda APC Ta Shirya Murɗe Zaben Gwamna

Jam'iyyar PDP Ta Tono Zargin Yadda APC Ta Shirya Murɗe Zaben Gwamna

  • Yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamna a jihar Ondo ranar Asabar, jam'iyyu na kara daura damara domin samun nasara
  • Jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Ondo ta yi zargin cewa APC ta haɗa kai da hukumar zabe ta kasa (INEC) domin mata murdiya
  • A yau mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima zai jagoranci jiga jigan APC domin gagarumin yakin neman zabe a Ondo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ondo - Yakin neman zabe na cigaba da ɗaukar dumi yayin da ranar zaben gwamna a Ondo ke kara matsowa.

Jam'iyyar PDP ta yi zargin cewa APC mai-ci ta shirya wani makircin yin maguɗi a zaben da ake shirin gudanarwa.

Shettima
Shettima zai jagoranci yakin neman zaben APC a Ondo. Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa sakataren yada labaran PDP, Kennedy Peretei ne ya fitar da sanarwa kan zargin maguɗin.

Kara karanta wannan

Jam'iyyu na shiri, INEC ta kai kayan zaben gwamnan jihar Ondo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP ta zargi APC da maguɗi a zaben Ondo

Sakataren yada labaran PDP, Kennedy Peretei ya yi zargin cewa akwai wani makirci da APC ta kulla domin yin maguɗi a zaben Ondo.

Kennedy Peretei ya ce shugaban APC, Abdullahi Ganduje ne ya haɗa kai da hukumar zabe domin tafka maguɗin.

"Mun gano wani shirin APC na maguɗi a zaben Ondo na ranar 16 ga Nuwamba.
Shugaban APC ya tura sunayen yan jam'iyyar biyu a kowace mazaba domin su shiga aikin zabe su yi maguɗi.
Muna kira ga al'umma da su shaida cewa APC ta shirya maguɗin ne saboda ta gaza tabuka komai."

APC ta karyata zargin jam'iyyar PDP

Vanguard ta wallafa cewa sakataren yada labaran APC, Alex Kalejaiye ya ce babu gaskiya a cikin zargin da PDP ta yi.

Kashim Shettima, Abdullahi Ganduje da sauran jiga jigan APC za su dura jihar Ondo domin gagarumin yakin neman zabe a yau.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: Matasan APC sun ba tsohon gwamna shawara kan takaddamarsa da EFCC

Obasanjo ya ziyarci jihar Ondo

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya kai ziyarar bude aiki jihar Edo yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamna a ranar Asabar.

A yayin ziyarar, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana yadda ya yi gwagwarmaya a lokacin da suke yakin neman shugabancin Najeriya a zaben 1999.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng