Malamin Addini Ya Fadi Hanyar da Su Atiku Za Su Bi Wajen Kwace Mulki a Hannun Tinubu a 2027
- Primate Elijah Ayodele ya samo mafita ga jam'iyyun adawa a yunƙurin da suke yi na ƙwace mulki a hannun Shugaba Bola Tinubu
- Shugaban cocin ya bayyana cewa dole sai sun yi haɗaka idan har sun son ganin sun raba Tinubu da mulkin Najeriya a shekarar 2027
- Malamin addinin ya bayyana cewa rashin haɗakar jam'iyyun adawan, za ta sanya Tinubu ya koma kan mulki cikin ruwan sanyi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya bayyana hanyar kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Primate Ayodele ya bayyana cewa haɗakar jam’iyyun siyasa ce kawai za ta iya raba Shugaba Tinubu da mulkin Najeriya a 2027.
Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Osho Oluwatosin ya sanya wa hannu, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace shawara aka ba ƴan adawa kan Tinubu
Primate Ayodele ya bayyana cewa idan manyan jam’iyyun adawa da suka haɗa da PDP, LP, da NNPP ba su haɗa kai ba, yunƙurinsu na lashe zaɓe ba zai haifar da ɗai mai ido ba.
Ya yi nuni da cewa akwai buƙatar dukkansu su haɗa kai su fitar da jajirtaccen ɗan takara, idan ba haka ba cikin sauƙi Tinubu zai samu tazarce a 2027, rahoton Daily Post ya tabbatar.
"Idan jam’iyyun PDP, LP, NNPP ba su haɗa kai ba, suka yi haɗaka sannan suka samar da jajirtaccen ɗan takara a zaɓen 2027, ba za su iya kawar da shugaba Tinubu ba."
"Cikin sauƙi shugaban ƙasa zai koma kan kujerarsa idan har ba a samu haɗaka mai ƙarfi daga manyan jam'iyyun siyasa ba."
"Idan PDP ta yanke shawarar tsayar da Atiku, za su faɗi zaɓe. A halin yanzu, babu wani gwamna mai ci a PDP da zai iya zama shugaban ƙasa a 2027, ba su da tasiri."
- Osho Oluwatosin
Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya caccaki Bola Ahmed Tinubu.
Atiku Abubakar ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya karbi mulki ne ba tare da wata manufar kawo cigaba ga ƴan Najeriya ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng