Dan TikTok Ya Fadi Yadda Matar Sanata a Arewa Ta ci Zarafinsa da Ya Soki Mijinta
- Yan Najeriya da dama sun soki matar sanata a jihar Taraba kan cafke matashi da kuma cin zarafinsa na tsawon kwanaki
- Matar Sanata Shuaibu Isa Lau ta umarci kama matashi mai suna Nafiu Hassan kan wallafa bidiyo kan halin da yankin Lau ke ciki
- Nafiu ya fadawa Legit Hausa yadda abin ya faru bayan fitar da wasu faifan bidiyo guda uku da ke da alaka da mazabar sanata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Taraba - Matar Sanata a jihar Taraba, Hajiya Fatima Lau ta sanya jami'an yan sanda sun kama wani matashi mai suna Nafiu Hassan.
Uwargidan Sanata Shuaibu Isa Lau da ke wakiltar Taraba ta Arewa ta kama matashin ne saboda sukar da ya yi wa mijinta kan rashin inganta harkokin lafiya da gyara hanya.
Matashi ya soki tabarbarewar shugabanci a Taraba
Matashin ya bayyana haka a cikin wani faifan bidiyo da Taraba Facts ta wallafa inda ya ke korafi kan samar da ruwan sha mai tsafta a yankin da yake wakilta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matashin ya bayyana ra'ayinsa kan wadannan matsalolin yankin, amma ya gamu da fushin matar sanatan.
Hakan ya sanya cafke shi wanda aka ci zarafinsa na kwanaki tare da zarginsa da ta yi na cin mutunci da kuma bata suna.
Rahotanni sun tabbatar da cewa jami'an yan sandan sun azabtar da matashin bayan kama shi, wanda hakan ya jawo magana a tsakanin al'umma.
Al'umma da dama sun bukaci a sake shi duba da take masa hakki na faɗin albarkacin baki da aka yi da doka ta ba shi a tsarin dimukradiyya.
Tattaunawar Legit Hausa ta ɗan TikTok
Nafiu Hassan ya ce ya yi bidiyo guda uku da suka shafi rashin tabuka wani abu a yankin Lau da ke jihar Taraba.
"Akwai bidiyo guda uku da na yi wanda ke da alaka da Lau, wata rana na fita aiki na ci karo da ita ta zo ta'azziya, kwatsam sai ga motoci guda uku suka sauka da cewa Hajiya tana son yin magana da ni."
"Kawai sai ta ce ku ci ubansu, da na ji haka sai na fara gudu inda suka fara mani ihun barawo, dana ji haka sai na tsaya, suka kama ni inda suka fara duka na har sai da na suma sannan suka bar duka na."
"Daga karshe, an saki mata biyu da muke tare da su da wani yaron gida na, amma ni aka ce sai na je gidan yari, a karshe dai saboda yaɗawa a kafofin sadarwa da shigar wasu manya aka sake ni da sharadin zan gode faya-fayen bidiyo."
"An bukaci na yi bidiyo na ba shi hakuri da cewa karya na ke yi na ce ba zan iya ba, daga baya a cikin ofishin aka fara goge na TikTok kafin zuwa kan Facebook."
- Nafiu Hassan
Daga karshe, matashin ya shaki iskar yanci
Daga bisani, matashin ya wallafa shakar iskar yanci da ya yi a shafinsa na Facebook inda ya yiwa al'umma godiya.
"Alhamdulillah, ina matukar godiya sosai kan jajircewar da kuka nuna min domin ganin na samu yanci."
"Nagode sosai Allah ya bar zumunci, sannan ina sanar da ku cewa zan yi hutu na kankanin lokaci domin samun hutu da jinyar da nake fama da ita."
- Nafiu Hassan
Kwamishina ya shiga matsala a Taraba
Kun ji cewa al'umma da dama a jihar Taraba sun caccaki wani kwamishina kan furucin da ya yi a kasar China wanda suke ganin abin takaici ne.
A cikin wani faifan bidiyo da ya karade kafofin sadarwa, an gano kwamishina, Habu James Philip yana cewa zai tabbatar da talauci a jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng