'Mun Yi Nadama': Kungiyar Arewa Ta Roki Tsohon Shugaban Kasa Ya Fito Takara a 2027
- Wata kungiyar Arewa, ACJ ta bayyana nadama kan kin zaben Jonathan a 2015, tana yabawa da irin ci gaban da ya kawo
- A taronta na Bauchi, ACJ ta jaddada yadda Jonathan ya tallafawa yankin Arewa ta hanyar inganta ilimi da walwalar jama’a
- Da wannan ne, kungiyar ta fara rokon tsohon shugaban kasar da ya sake fitowa takarar shugaban kasa a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bauchi - Kungiyar Arewa Consensus for Jonathan (ACJ), babbar ƙungiya ta siyasar Arewa, ta bayyana nadamar kin zaben tsohon shugaba Goodluck Jonathan a 2015.
A zaɓen shekarar 2015, Jonathan ya sha kaye a hannun tsohon shugaba Muhammadu Buhari bayan gaza samun goyon baya daga 'yan Arewa Arewa.
Kungiyar Arewa ta fara zawarcin Jonathan
Kungiyar da ta ki zaben Jonathan a wancan lokacin yanzu ta yarda cewa jagorancinsa zai iya kasancewa mafi amfani, a cewar rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce yayin da ƙalubalen tattalin arziki ke ƙaruwa a ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu, yankin Arewa sun fara bayyana goyon bayansu ga Jonathan a fili.
ACJ ta gudanar da taron manema labarai a Bauchi a ranar 10 ga Nuwamba, inda ta tattauna ribar da Arewa ta samu a lokacin mulkin Jonathan.
Kungiyar ta lura cewa Jonathan ya mayar da hankali kan ci gaban al'umma a yankin, wanda hakan ya kawo ci gaba mai ma’ana a Arewa.
'Arewa ta ji dadin mulkin Jonathan' - ACJ
Manniru Musa Yisin, shugaban ACJ na ƙasa, ya bayyana cewa jama’ar Arewa sun ji dadin mulkin Jonathan, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Yisin ya yaba da shirye-shiryen Jonathan da suka mayar da hankali wajen shawo kan matsalolin yankin, musamman bunkasa rayuwar al'umma da ilimi.
A cewar Yisin, gwamnatin Jonathan na da fahimtar muhimmancin ilimi wajen bunƙasa mutum da ƙasa baki ɗaya.
Ya ambaci shirin Almajiri Education Initiative a matsayin wani tsari da ya magance doguwar matsalar ilimi a Arewa, wanda ya samu karɓuwa sosai.
Kungiya ta kwatanta Tinubu da Jonathan
Kungiyar ta bambanta jagorancin Jonathan da na Tinubu, inda ta ce Tinubu bai fito da manufofin da suka shafi muhimman batutuwan yankin ba
Yisin ya ci gaba da suka kan gwamnatin Tinubu, yana danganta ƙuncin tattalin arziki da talauci ga abin da ya kira “manufofi marasa amfani.”
Ya ƙara da cewa manufofin haraji na yanzu sun kara wahalar da rayuwar mutane, da dama daga cikin ‘yan Arewa na cikin talauci.
Yayin da yake kira ga Jonathan da ya tsaya takara a 2027, Yisin ya nuna tabbacin cewa Jonathan zai iya haɗa kan Najeriya ta hanyar kwarewarsa kan matsalolin Arewa.
2027: Malami ya ba Jonathan shawara
A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen fasto a Najeriya, Elijah Ayodele ya gargadi tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan kan tsayawa takara a 2027.
Ayodele ya ce bai kamata Jonathan ya biyewa masu neman tunkuda shi tsayawa takara ba a 2027, ya bukaci tsohon shugaban da ya kare martabar da ya ke da ita a kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng