Ministan Buhari Ya Gano Dalilin Tinubu na Nada Wata Minista, Ya Bukaci Korar Ministoci 3
- Tsohon Minista a mulkin Muhammadu Buhari ya koka kan tsarin garambawul na gwamnatin Bola Ahmed Tinubu
- Solomon Dalung ya ce an yi garambawul din ne saboda siyasa ba tare da korar wadanda suka kamata a cire ba
- Tsohon Ministan ya ce ya kamata a sallami akalla 70% na Ministoci duba da yadda suka gaza yin katabus a ma'aikatunsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Plateau - Tsohon Ministan wasanni da matasa, Solomon Dalung ya koka kan garambawul a gwamnatin Bola Tinubu.
Solomon Dalung ya ce babu wani garambawul da aka yi illa Bola Tinubu ya yi sauye-sauye ne saboda zaben 2027.
Dalung ya soki Tinubu game da garambawul
Tsohon Ministan ya bayyana haka ne a daren jiya Litinin 11 ga watan Nuwambar 2024 a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar, Dalung ya ce Tinubu ya nada Bianca Ojukwu ne domin yaudarar yankin Kudu maso Gabas saboda zaben 2027.
Ya ce babu wani garambawul kawai shirin siyasar 2027 ake yi inda ya ce an kori wasu Ministoci ne saboda ba su da kusanci da Tinubu.
Dalung ya kara da cewa idan har garambawul na gaskiya ne kusan 70% na Ministoci ya kamata a kora.
'Ministocin da ya kamata a kora'- Dalung
Tsohon ministan a mulkin Muhammadu Buhari ya jero Ministoci da ya kamata a kora ciki har da Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Ya ce Wike ba shi da da'a ko kadan, bai mutunta mutane ko gwamnati a lokacin da aka fi bukatar zaman lafiya.
Sannan ya yi mamakin barin Ministan tsaro yayin da yan ta'adda ke cin karensu babu babbaka a Arewa.
Har ila yau, Dalung ya bukaci korar Ministan makamashi duba da yadda wutar lantarki ta rika lalacewa cikin yan kwanaki ƙadan musamman a Arewacin Najeriya.
Solomon Dalung ya magantu kan zanga-zanga
Kun ji cewa tsohon Ministan wasanni da matasan Najeriya, Solomon Dalung ya caccaki malaman addini kan kokarin hana zanga-zanga.
Dalung ya ce yanzu da aka kara kudin mai da yawansu da kafa za su rika yawo saboda haka da kansu za su shiga zanga-zanga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng