'Juyin Juya Hali na Tafe': Tsohon Gwamna a APC Ya Gargadi Tinubu, Ya Kawo Mafita

'Juyin Juya Hali na Tafe': Tsohon Gwamna a APC Ya Gargadi Tinubu, Ya Kawo Mafita

  • Tsohon gwamna a jam'iyyar APC ya yi gargadi kan yiwuwar samun juyin-juya-hali a Najeriya saboda halin kunci da ake ciki a kasar
  • Rauf Aregbesola ya koka kan yadda tattalin arziki da cigaban siyasa ke samun koma baya a kullum inda ya ce babban hatsari ne
  • Tsohon gwamnan jihar Osun ya shawarci gwamnatoci su dauki matakin shawo kan matsalolin kafin juyewa zuwa wani abin daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun - Tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola ya yi magana kan halin kunci da ake ciki a Najeriya.

Rauf Aregbesola ya ce idan ba a dauki matakin gaggawa ba za a iya fadawa juyin-juya-hali a Najeriya saboda babu wata hanyar tsira.

Tsohon gwamna ya yi gargadi kan yiwuwar juyin juya hali a Najeriya
Tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola ya ce za a iya fuskantar juyin juya hali a kasa. Hoto: Rauf Aregbesola.
Asali: Facebook

Aregbesola ya koka kan halin kunci a Najeriya

Tsohon gwamnan ya fadi haka ne a jiya Litinin 11 ga watan Nuwambar 2024 inda ya koka kan rugujewar tattalin arziki, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Daurarru sun ji labarin matsin rayuwa a waje, an samu masu murna da zaman kurkuku

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aregbesola ya ce kullum Najeriya kara samun koma baya take yi duba da rata da ke tsakanin masu hali da talakawa a kasar.

Ya ce matsin tattalin arziki da kuma rashin tabbas kan halin da za a sake shiga shi zai halatta juyin-juya-hali cikin sauki a kasa, The Guardian ta ruwaito.

Aregbesola ya yi hasashen juyin juya hali

"Mun ga yadda matsin tattalin arziki da rashin cigaban siyasa ya jefa al'umma cikin mummunan yanayi kowa ya sani."
"Arziki yana hannun yan tsiraru a yanzu, da a ce babu matsala da ba za mu zo nan muna maganganu ba, hakan ya nuna muna cikin babbar matsala."
"Duk abin da ba zai ba al'umma yanci ba, dole za su yi tawaye, idan abubuwa suka kara lalacewa dole a samu juyin-juya-hali a kasa."

- Rauf Aregbesola

APC ta dakatar da tsohon gwamna, Aregbesola

Kun ji cewa jam'iyyar APC reshen jihar Osun ta dakatar da tsohon gwamna, Rauf Aregbesola daga cikinta saboda wasu zarge-zarge.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya karfafi yan Najeriya, ya yi kyakkyawan albishir

Jam'iyya mai mulki ta ɗauki matakin ne kan tsohon gwamnan kan wasu zarge-zarge da suka shafi zangon-kasa da cin amanarta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.