Jam'iyyar Kwankwaso Ta Rikice, Saɓani Ya Gifta Tsakanin Manyan NNPP
Rikicin da ya kutsa jam'iyyar NNPP a yan kwanakin nan ya na ƙara ƙamari yayin da aka samu ƙarin jigo a jam'iyyar da samun rashin jituwa da shugabansu, Dr. Hashimu Dungurawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Sanata Kawu Sumaila ya yi martani kan kalaman shugaban NNPP na Kano, Dr. Hashimu Dungurawa tare da shawartar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da gwamna Abba Kabir Yusuf su yi hankali da shi.
Kawu Sumaila ya zama babban jigo na uku a NNPP da ke takun saka da Dr Dungurawa tare zargin cewa zai ia kashe tafiyar Kwankwasiyya baki dayanta.
Rikicin cikin gida a jam'iyyar NNPP
Baya ga bangaren Hashimu Dungurawa na Kwankwasiyya, akwai tsagin Barista Dalhatu Shehu da ke da'awar su ne asalin yan NNPP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da dai Sani Aliyu Madakin Gini bai furta cewa ya koma wancan tsagin ba, amma ya bayyana barin tsagin Kwankwasiyya.
Legit ta tattaro jerin manyan NNPP da ke samun sabani da jagorancin jam'iyyar a Kano, farawa da na baya-bayan nan, Kawu Sumaila.
1. "Na ba Kwankwasiyya gudunmawa:" Kawu Sumaila
Tun bayan wasu kalamai da Sanata Kawu Sumaila ya yi a matsayin shawara ga gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ne shugaban NNPP, Hashimu Dungurawa ya dura kansa.
Dungurawa na ganin kalaman Kawu Sumaila ba su dace ba, domin Abba Kabir Yusuf ba shi da hurumin korar wasu da ake zargin sun dauki nauyin tafiyar 'Abba tsaya da kafarka'.
Da alama martanin Dr. Dungurawa sun yi wa Sanata Kawu Sumaila zafi, inda ya fito ya na bayyana irin gudunmawar da ya bayar a tafiyar Kwankwasiyya da nasarar gwamnan Kano.
A martanin nasa, Kawu Sumaila na ganin Hashimu Dungurawa zai yi wa tafiyar Kwankwasiyya da gwamna Abba illa matuka.
2. Hon. Madakin Gini ya fice daga Kwankwasiyya
Bidiyon dan majalisa mai wakiltar Dala, Aliyu Sani Madakin Gini ya fitar na ficewa daga Kwankwasiyya ya dauki hankulan jama'a.
Abin da ya fi kara daukar hankali shi ne yadda ya bayyana cewa har yanzu ya na nan daram a cikin jam'iyyar NNPP, tafiyar Kwankwasiyya ce ba zai kara yi ba.
A kalaman Madakin Gini;
"Kwankwasiyya ƙarya ce, Kwankwasiyya yaudara ce."
A wata hira da ya yi da BBC, wakilin mutanen Dala ya zargi jagoran Kwankwasiyya, Rabi'u Musa Kwankwaso da son kansa da kuma gina tafiyar saboda ƙashin kai.
3. Rurum ya bar Kwankwasiyya
Dan majalisa mai wakiltar ƙananan hukumomin Kibiya da Rano da Bunkure, Hon. Kabiru Alhassan Rurum shi ne jagora a NNPP na uku da ya fice daga Kwankwasiyya.
A zargin da ya yi, ya zargi tsagin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da rashin adalci da nuna son kai, kuma ya na ganin ba zai iya cigaba da zama a tsarin ba.
Wannan ya kawo adadin ƙusoshin NNPP da su ka barranta kansu da tafiyar tsagin Hashimu Dungurawa zuwa uku, sai dai har yanzu Kawu Sumaila bai barranta da Kwankwasiyya ba kai tsaye.
Kwankwasiyya ta yi martani ga yan majalisa
A wani labarin kun ji cewa kungiyar Kwankwasiyya ta kasa reshen jihar Kano ta ce fitar wasu yan majalisa daga tafiyar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ba zai rage su ba.
Shugaban tafiyar Kwankwasiyya a jihar Kano, Dr. Musa Gambo Hamisu Dan Zaki ya ce bai ga amfani dashi cewar yan majalisar daga Kwankwasiyya ba amma su na NNPP.
Dr. Musa Gambo Hamisu Dan Zaki ya kara da cewa Kwankwasiyya ce ta amfani yan majalisar kuma fitarsu ba zai zama nakasu ga tafiyarsu tsohon gwamna, Rabi'u Musa Kwankwaso ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng