'Akwai Riba': Gwamna Ya Fadi Yadda Rikicin da Ke Faruwa a jiharsa Ya Zama Alheri
- Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara ya yi magana kan rigimar siyasar da ke faruwa a jihar tun farkon hawansa mulki
- Fubara ya ce a wurinsa hakan alheri ne saboda Ubangiji ya kawo rigimar domin sauya akalar jihar baki daya
- Hakan na zuwa ne yayin da Fubara ke cigaba da takun-saka tsakaninsa da mai gidansa Ministan Abuja, Nyesom Wike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara ya yi magana kan rigimar siyasar da ke faruwa a jihar Rivers a Kudancin Najeriya.
Fubara ya ce rigimar siyasar da ta bullo alheri ne ga jihar domin ta samar da yancin siyasa da bunƙasar tattalin arziki.
Gwamna Fubara ya magantu kan rikicin Rivers
Gwamnan ya bayyana haka ne a yau Lahadi 10 ga watan Nuwambar 2024 yayin taro da sarakunan gargajiya, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fubara ya ce rikicin daga Ubangiji ya ke domin ba jihar wasu hanyoyin cigaba da ba a yi tsammani ba.
Daga bisani, Fubara ya ce samun cigaba da yake yi a jihar ya dogara ne da Ubangiji da mika lamuransa gare shi, Punch ta ruwaito.
Fubara ya fadi alheri cikin rigimar Rivers
"Na yi imanin abin da kuke cewa rigima ne, ni ba haka ba ne a gare ni saboda ya kawo sauyi a siyasa da tattalin arzikin jihar Rivers."
"Ina ganin hakan kaman hikimar Ubangiji ne domin sauya akalar jihar Rivers daga kan turbar da take."
"Tun farkon fara wannan rigima, Ubangiji yana kara kaimu gaba, madadin samun nakasa kullum kara ƙarfi muke yi."
- Siminalayi Fubara
INEC ta tsoma baki a rikicin jihar Rivers
Kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta bayyana cewa ta rasa yadda za ta yi da rikicin majalisar dokokin jihar Ribas.
Shugaban INEC, Mahmud Yakubu ya ce kowane ɓangare ya buƙaci a maye gurbin abokan hamayyarsa, sannan kuma kotuna na cin karo da juna.
Farfesa Mahmud ya ce a halin yanzu dai INEC na bibiyar abubuwan da ke faruwa a majalisar amma ba za ta iya yin komai ba.
Asali: Legit.ng