Atiku Ya Fadi Mutum 1 da Ya Yi Kokarin Sulhunta Shi da Obasanjo Lokacin Mulkinsu
- Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar ya fadi wanda ya yi kokarin sulhunta shi da Olusegun Obasanjo
- Atiku ya yabawa halayen tsohon shugaban NDDC, Cif Onyema Ugochukwu kan irin kokarin sulhu da ya yi a tsakaninsa da Obasanjo
- Atiku ya tuno irin dattaku da Ugochukwu ya nuna ba tare da nuna bangare ba inda ya ce tabbas mutum ne mai kishin kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi magana kan rigimarsa da Olusegun Obasanjo.
Atiku ya yabawa rawar da tsohon shugaban NDDC, Cif Onyema Ugochukwu ya taka wurin sulhunta su.
Matsalolin da Atiku ya samu da Obasanjo
Dan takarar PDP a 2023 ya fadi haka ne yayin bikin cika shekaru 80 da Ugochukwu ya yi a duniya a Abuja, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ba a manta ba, Obasanjo da Atiku sun yawaita samun matsaloli a tsawon mulkinsu daga shekarar 1999 zuwa 2007.
Atiku da mai gidansa ba su ga maciji musamman bayan samun nasara a karo na biyu a shekarar 2003.
Yadda dattijo ya yi kokarin sulhunta su
Sai dai Atiku bai manta da rawar da Ugochukwu ya taka ba a wancan lokaci inda ya ce mutum ne mai kishin Najeriya.
Atiku ya ce kwata-kwata Ugochukwu bai nuna bangaren da ya fi so ba illa ya kasance kawai mai kokarin sulhu a tsanani.
"Ba zan iya cewa na san Ugochukwu sosai ba, kawai mun hadu da shi ne a shekarun 1998 zuwa 1999, amma tun daga wancan lokaci muka cigaba da mu'amala har zuwa yanzu."
"A wancan lokaci da muke samun matsala tsakani na da Obasanjo, ya yi kokarin sulhu ba tare da nuna bangaren da yake ba."
- Atiku Abubakar
Obasanjo ya magantu kan jam'iyyar siyasa
Kun ji cewa tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ce kwata-kwata bai da wata jam'iyyar siyasa da yake goyon baya.
Cif Obasanjo ya bayyana cewa shi a yanzu bai da jam'iyya yana nan a matsayin dan kasa da bai da alaka da jam'iyyar siyasa.
Tsohon shugaban kasar ya koka kan yadda yan kasa ke fuskantar matsaloli daban-daban inda ya ce akwai haske a gaba.
Asali: Legit.ng