Atiku ya bayyana musabbabin rikicin dake tsakaninsa da Obasanjo
- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana yanda aka yafice shi daga gwamnatin Obasanjo a mulkinsa na biyu
- Atiku yace rashin jituwarsu ya soma ne tun lokacin da ya nuna rashin amincewa da ra’ayin tsohon shugaban kasar kan tsawaita mulkin shugabanci
- Ya kara da cewa rashin amincewarsa kan dokar tsawaita mulkin shugaban kasa ba komai bane illa ganin an baiwa matasa damar shugabanci
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kara haske kan rashin jituwar dake tsakanin shi da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a gwamnatinsu a karo na biyu.
Atiku ya bayyana cewa an yafice shi daga gwamnatin bayan ya nuna rashin amincewa ga ra’ayin Obasanjo kan tswaita shugabancin kasa a lokacin mulkinsa na biyu.
KU KARANTA KUMA: Rahama Sadau ta yi bukin zagayowar ranar haihuwarta a kasar Cyprus (hoto)
Atiku ya bayyana hakane yayinda yake mayar da martani ga bayyananniyar wasika da wani mai wasan barkonci , Francis Agoda, wanda aka fi sani da I Go Dye ya rubuta masa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng