Zaben Amurka: APC Ta Fadi Abin da Zai Faru a 2027, Ta Bayyana Lokacin Shan Romo

Zaben Amurka: APC Ta Fadi Abin da Zai Faru a 2027, Ta Bayyana Lokacin Shan Romo

  • Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta yi kaca-kaca da jam'iyyun adawa a kasar musamman kan zaben Amurka
  • APC ta ce tana da tabbacin Tinubu ne zai lashe zaben 2027 inda ta ce yan adawa ba su shirya kansu ba tukuna
  • Wannan na zuwa ne bayan Kamala Haris da ke kan mulki ta yi rashin nasara a hannun Donald Trump dan adawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jam'iyyar APC ta yi magana kan zaben Amurka inda Kamala Haris ta yi rashin nasara.

APC ta bugi kirji inda ta gargadi yan adawa a Najeriya ka da su yaudari kansu game da zaben Amurka.

APC ta bugi kirji kan lashe zaben 2027
Jam'iyyar APC a Najeriya ta sha alwashin lashe zaben 2027. Hoto: Bayo Onanuga.
Asali: Twitter

Jam'iyyar APC ta magantu kan zaben Amurka

Kara karanta wannan

Ana daf da zabe, yan APC sun watsawa Gwamna kasa a ido, sun goyi bayan dan adawa

Daraktan yada labaran jam'iyyar, Bala Ibrahim ya ce akwai bambanci tsakanin hukumomin zaben Amurka da na Najeriya, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ibrahim ya ce kawai domin Haris da ke mulki ta fadi zabe ba shi ke nuna Tinubu zai samu matsala a 2027 ba.

Ya ce abin da ke faruwa bai dadara jam'iyyar APC ba inda ya ce hatta su yan adawar ma kansu a rabe yake.

APC ta bugi kirji kan zaben 2027

"Yadda APC ke aiki tukuru da kawo tsare-tsare da suke da tsauri a farko, za mu ci moriyar hakan nan kusa."
"Tsakanin 2026 zuwa 2027 za mu fara cin gajiyar tsare-tsaren a lokacin ne yan Najeriya za su fara yiwa Tinubu godiya ana daf da zabe."
"Babu yadda za a yi wani daga waje wanda ya gaza gyara kasa ya zo ya ce zai kada gwamnati mai ci, Tinubu da APC sun san iya shegen da yan adawa ke yi duka."

Kara karanta wannan

Jill Stein da ‘yan takaran da suka nemi mulkin Amurka tare da Trump da Harris

- Bala Ibrahim

PDP ta yi magana kan zaben 2027

Kun ji cewa Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya caccaki tsarin jam'iyyar APC wurin kakabawa al'umma halin kunci.

Makinde ya bayyana cewa zaben Najeriya a 2027 ya rage tsakanin jam'iyyar APC da kuma al'ummar kasar.

Ya ce gwamnatin APC ta rikita kasar da talauci da rashin iya mulki tun bayan karbar ragamar Najeriya a zaben 2015.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.